Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar tsaro ta civil defence za ta bada cikakken tsaro a lokacin gudanar da bukukkuwan sallah.
Kwamandan hukumar a Katsina Aminu Ahmad ya sanar da haka a hira da manema labarai kan shirye shiryen da hukumar tayi na samar da tsaro a jihar.
Ya ce hukumar za ta tabbatar da kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar da kuma ganin anyi hidimar sallah cikin kwanciyar hankali.
Har ila yau kwamandan hukumar ya ce jami’an sa zasu kare duk kaddarorin gwamnati da ke faɗin jihar.
Ya jaddada ƙudirin babban kwamanda na ƙasa Abubakar Audi na kare rayuka da dukiyar al’ummar kasar a lokacin bukukuwan sallah.
Aminu Ahmad ya umarci jami’an tsaron da su rinƙa tattare sahihin bayanai na sirri da kuma haɗa kai da sauran jami’an tsaro domin tabbatar ta tsaro a jihar.
Ya bayyana haka a fadar sarakunan Katsina da Daura a matsayin wuraren da hukumar za ta girke jami’an ta domin su tabbatar anyi hawan sallah da hawan bariki lafiya .
“Haka kuma wuraren da za a gudanar da sallar Eid-el-fitr a duk ƙananan hukumomi 34 a jihar za su sami kulawa na jami’an tsaron”inji kwamandan.
Sai yayi kira ga jami’an tsaron da su nuna ƙwarewa a yayin gudanar da aikin su da kuma haɗa kai da sauran jami’an tsaro wajen tabbatar da tsaro a jihar.
Kwamandan ya kuma kira ga al’ummar jihar da su ba jami’an tsaron haɗin kai don ganin an gudanar da hidimar sallah cikin kwanciyar hankali.
