Kisan Edo: Gwamnatin Kano ta yi alla-wadai da neman a yi adalci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Jihar Kano ta jajenta wa iyalai da abokan waɗanda iftila’in Uromi ya afka masu a Jihar Edo.

Kisan gillar ya yi sanadin mutuwar kimanin mutane 16, lamarin da ke da buƙatar shigar hukuma da ɓangaren harkokin shari’a.

Lamarin ya auku ne a lokacin da wasu mafarauta suka taho daga Jihar Ribas domin zuwa Jihar Kano yin bikin Sallah tare da iyalansu, inda wasu ƴan bijilante da wasu matasa ɗauke da makamai suka tsare su, sannan suka musu duka tare da ƙone su baki ɗaya.

A sanarwar da Kwamishinan Labarai da Wayar da kan al’umma na jihar, Abdullahi Ibrahim Waiya ya fitar, Gwamna Abba ya ce kisan mafarautan ya nuna yadda al’umma su ke bijirewa doka da oda da rashin tausayin ran ɗan-adam.

Don haka ne ya ke kira da a gaggauta gudanar da bincike mai zurfi tare da ɗaukar matakan da suka dace ga waɗanda ke da hannu a lamarin.

Ya kuma yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Monday Okpebholo na jihar da su tabbatar da adalci ta hanyar gurfanar da waɗanda suke da hannu a ɗanyen aikin tare da hukunta su a dokance.

By Babaji