
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar Sojojin ƙasa ta ɗora musabbabin rikicin da ya faru a Abuja tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro akan masu zanga-zangar, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 12.
A ranar Juma’a ne aka gudanar da zanga-zangar ƙarƙashin ƙungiyar Shi’a ta IMN da aka dakatar, waɗanda suka yi taron ranar Ƙudus da nufin shiga sahun masu gangamin goyon bayan Palastine.
Wani rahoton sirri ya ce, 11 daga ƴan zanga-zangar da soja ɗaya ne suka rasa rayukansu a yayin karambattar.
Ƙungiyar Amnesty International a Nijeriya ta ce sojojin sun yi harbe-harbe ne acikin ƴan zanga-zangar a yunƙurinsu na kula da dandazon da hana aukuwar rikici.
Kakakin sojojin, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu ya bayyana cewa, ganin haka ne ya sa ƴan zanga-zangar suka fara tada hayaniya da ƙoƙarin takalar jami’an tsaron, lamarin day juya zuwa tarzoma da hallaka rayukan wasu daga ciki.
Tun a shekarar 2019 ne aka dakatar da ayyukan IMN kasancewar ta fi mayar da hankali akan gudanar da zanga-zanga, lamarin da ya sa hukumomin tsaro suka nemi a dakatar da ita.
A watan Agusta ne harin mambobin IMN ya yi sanadiyyar mutuwar ƴan sanda biyu a Abuja.
