Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya halarci sallar Idi tare da mai martaba Sarkin Gombe, Alhaji (Dokta) Abubakar Shehu Abubakar III, CFR, da sauran musulmi a ranar Lahadi, don kammala azumin watan Ramadan.
An gudanar da sallar mai raka’a biyu a babban masallacin Bubayero, inda limamin masallacin, Ustaz Aliyu Hammari, ya jagoranci sallar.
Gwamnann ya yi Kira ga haɗin Kai, addu’o’i don zaman lafiya, da matakai masu ƙarfi kan matsalar banagar siyasa ta Kalare.
“An kammala Ramadan, amma darussansa sun rage mana. Mu ci gaba da bin ruhin sadaukarwa, ƙauna, da tausayi. A matsayinmu na mutane da gwamnati, muna da nauyin tallafa wa masu buƙata. Idan muka ci gaba da wannan, za mu taimaka wajen rage raɗaɗin wahalhalun da jama’a ke fuskanta,” in ji gwamnan.
Gwamnan ya bukaci jama’a su ci gaba da addu’o’i don zaman lafiya da ci gaban Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya. Haka kuma, ya gode wa malamai da al’umma bisa addu’o’in da suka gudanar a tsawon watan Ramadan, yana mai cewa haɗin kai da ƙoƙari tare suna da matuƙar muhimmanci wajen samun zaman lafiya da cigaba.
Da yake magana kan matsalar tsaro, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana matakan da gwamnatinsa ke ɗauka don magance matsalar matasa masu tayar da hankali, wato Kalare.
Inda ya bayyana cewa gwamnatin ta ba da gudunmawar motocin aiki guda 50 ga hukumomin tsaro don ƙarfafa ayyukansu na yaƙi da laifuka a jihar. Ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma, iyaye, da sauran masu ruwa da tsaki su haɗa kai da gwamnati wajen samar da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa.
A wani ɓangare na bikin Sallah, Gwamnan ya jagoranci manyan baƙi zuwa fadar sarkin Gombe don halartar bikin hawan sallah na Jafi.
A wajen taron, mai martaba Sarkin Gombe, Alhaji (Dokta) Abubakar Shehu Abubakar III, CFR, ya yi kira ga zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya, yana mai cewa ya zama dole su zauna lafiya don gujewa rikici.
Ya kuma tabbatar da jajircewar masarautar wajen tallafa wa gwamnatin jihar don tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da ci gaba.
Gwamna Inuwa Yahaya ya sake jaddada ƙudurinsa na inganta jin daɗin al’ummar Jihar Gombe ta ayyuka da shirye-shiryen da suka shafi al’umma tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
