
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar tabbatar da gaskiya da adalci kan zamantakewa (SERAP), ta yi kira ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas da su gaggauta janye ƙudirin neman tasa ƙeyar waɗanda ba su yi zaɓe ba a matakin jiha ko tarayya zuwa gidan yari na wata shida da kuma ko ƙaƙaba masu tarar N100,000.
A ranar Asabar ne ƙungiyar ta kare haƙƙin ɗan-adam, a wata takarda daga Mataimakin Daraktanta, Kolawole Oluwadare ta bayyana hakan da cewa za ta ƙalubalanci ƙoƙarin tabbatar da ƙudirin a kotu matuƙar ba su janye shi ba.
Ta ce, ƙoƙarin hukunta waɗanda ba sa yin zaɓe ko suka ƙi yi a wani lokaci, ya saɓa wa doka kuma bai da wata muhimmanci.
SERAP ta kuma ce, doka ta bada ƴancin yin zaɓe, amma hakan ba shi ke nuna tilas ne yin hakan ba, don ɗan ƙasa ya na da ƴancin yi ko kuma akasin hakan.
Haka kuma, ƙudirin ya saɓa wa doka ta 14(1)(c) ta kundin dokar ƙasa da ke magana akan ƴancin shiga siyasa da saɓa wa wasu dokoki a mataki na ƙasa da ma Afirka baki ɗaya.
Bugu da ƙari, ta yi kira ga majalisun da su yi kwaskwarima ga dokokin ƙasa da na zaɓe ta yadda za a bada dama ga mai zaɓe ya yi rajista ta yanar gizo da kuma gudanar da sauran al’amuran da suka shafi zaɓen a zamanance.
