Kano da Legas na gaba a yawan masu katin ɗan ƙasa

Spread the love

Hukumar kula da shaidar ɗan ƙasa (NIMC) ta bayyana cewa adadin ‘yan Najeriya da suka yi rijistar lambar shaidar ɗann ƙasa (NIN) ya kai miliyan 117 zuwa ranar 28 ga Fabrairu, 2025. Bisa ga alkaluman da hukumar ta fitar, maza sun fi mata yawan rijista da kashi 56.5% (miliyan 66.2), yayin da mata ke da kashi 43.5% (miliyan 51).

Jihar Legas ce ta fi kowacce yawan masu rijista da fiye da miliyan 12.6, yayin da Kano ke biye da miliyan 10.2. Sauran jihohin da ke sahun gaba sun haɗa da Kaduna (miliyan 6.9), Ogun (miliyan 4.9), da Oyo (miliyan 4.5). A ɗaya ɓangaren, jihohin da suka fi ƙarancin rajista sun haɗa da Bayelsa (758,111), Ebonyi (990,775), da Ekiti (1,143,102).

Rahoton ya kuma nuna cewa yankunan Arewa da Kudu suna da kusan yawan rijista iri ɗaya. Sauran jihohin da ke da ƙarancin rijista sun hada da Kurus Ribas, Taraba, Yobe, Kogi, Enugu, Kwara, da Imo. Wannan ci gaba yana nuna yadda ‘yan Najeriya ke ƙara fahimtar muhimmancin samun NIN domin amfani da shi a muhimman ayyukan gwamnati da na kasuwanci.

By ukarofi