Wasu mazauna garin Uromi da ke Jihar Edo, musamman yankunan Old Ilushi Road, Opere, da Good Will Junction, sun fara barin gidajensu saboda tsoron ramuwar gayya da kuma kame da jami’an tsaro ke yi. Wannan na zuwa ne bayan da wasu matasa suka kashe matafiya 16 daga Arewa a yankin a ranar Alhamis da ta gabata.
Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya kai ziyara Kano inda ya tabbatar wa da al’ummar Arewa cewa za a yi adalci ga waɗanda aka kashe. Ya kuma bayyana cewa an kama mutane 14 da ake zargi da hannu a lamarin, kuma za a kai su Abuja domin ci gaba da bincike.
Wasu mazauna yankin sun ce tun bayan aukuwar lamarin, mutane sun daina fita gona saboda tsoron abin da zai biyo baya. Har ila yau, an samu rahoton cewa ‘yan sanda na ci gaba da kama mutane, inda wani matashi da ke kan babur aka cafke kusa da Opere Secondary School, duk da cewa ya ce bai da masaniya game da abin da ya faru.
A wani yanki na kusa, Ekpoma, an samu ruɗani a kasuwar garin bayan wani jita-jita da ya karaɗe gari cewa wasu ‘yan bindiga na shirin kai hari. Hakan ya sa direbobi suka juya motocinsu domin tsira. Sai dai daga bisani, jami’an tsaro sun garzaya yankin domin tabbatar da doka da oda.
