
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamna Monday Okpebholo ya yi alla-wadai da kisan wulaƙancin da aka yi wa mafarauta 16 a yankin Udune dake Ƙaramar Hukumar Uromi a Jihar Edo, ya na mai cewa ba za su bari ya tafi a banza ba.
Gwmanan ya faɗi hakan ne a yayin ziyarar ta’aziyya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da al’umma a Gidan Gwamnatin Jihar Kano, ranar Litinin.
Okpebholo ya bayyana alhininsa a lokacin da ya haɗu da al’ummar Hausawa, waɗanda ya ce sun taimaka masa a lokacin yaƙin neman zaɓensa da ma lokacin da aka gudanar da zaɓen watanni kaɗan da suka gabata.
Ya kuma ce, Shugaba Bola Tinubu ya umarci Sufeton ƴan sanda da wasu hukumomin tsaro da su bi diddigi tare da kamo waɗanda ke da hannu acikin aikata laifin tare da hukunta su a hukumance.
Ya ce, sun ƙaddamar da matakan tsaro don tabbatar da kamo duk wanda aka samu da hannu a laifin.
Ya ƙara da cewa, irin aikin ya saɓa wa ƙa’idar zamantakewa da karantarwar addinin Musulunci da na Kiristanci.
A halin yanzu an kama mutane 14 bisa zargin su da hannu a faruwar al’amarin, inji Okpebholo.
A nasa jawabin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jinjina wa Okpebholo ganin yadda ya yunƙura wajen ɗaukar matakan tsaro biyo bayan aukuwar lamarin, ya na mai cewa sun ɗauki matakan da suka dace wajen ganin al’umma ba su ɗauki doka a hannunsu ba.
Ya kuma yi kira da a gabatar da waɗanda aka kama a bainar jama’a don rage wa iyalan waɗanda abin ya shafa raɗaɗi da kuma tabbatar da adalci.
