Mataimakin Shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima ya isa ƙasar Senegal domin wakiltar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yayin da ƙasar ke bikin cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai.
Inda yake tare da ƙaramin ministan harkokin waje Ambassador Bianca Odumegwu Ojukwu da Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da harkokin waje, Hon Oluwole Oke,yayin da suka sauka a filin jirgin sama na Dakar dake Senegal.
Wannan na zuwa ne biyo bayan gayyatar da Shugaban ƙasar ta Senegal Bassirou Diomaye Faye ya aike wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinibu domin gudanar da bikin ranar ‘yancin kai wanda zai gudana a gobe Juma’a.
Ana sa ran dawowar sa gida Najeriya bayan kammala gudanar da bikin.
