
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Alhamis ne Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce zai halarci ta’aziyyar rasuwar baki ɗaya waɗanda ke masa fatan mutuwa.
Ya faɗi hakan ne sakamakon jita-jita da ake yaɗawa na cewa ya yanki jiki a yayin wani zama a Abuja a makon da ya gabata, inda aka garzaya da shi Faransa, daga bisani kuma ya rasu.
Saidai, a yayin ganawa da manema labarai bayan kammala duba wasu ayyuka a Abuja, Wike ya ce an yi ta yaɗa batun mutuwarsa ne da nufin hana shi cigaba da ayyukan da ya sa a gaba.
A cewarsa, magautansa na siyasa ne suka ƙirƙiro zancen ƙaryar bayan zargi akan dakataccen Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara da tsohon shugaban ma’aikatan jihar, George Nwaeke ya yi.
Wike ya ce, lallai ya fi wasu daga cikin waɗanda suka fitar da batun lafiya, ya na mai cewa zai rubuta saƙon ta’aziyyarsu.
Ya kuma ce, bai ko nuna alamar rashin lafiya ba, balle ya yanki jiki, don haka ne ya ce ko sau ɗaya hakan bai taɓa faruwa da shi ba.
