Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da asusun gwamnati ya sake ƙwato dalar Amurka miliyan 14.2 (kimanin Naira biliyan 21.4) daga wasu kamfanonin mai da iskar gas guda huɗu a ci gaba da gudanar da bincike kan matsalar kuɗaɗen shiga a fannin man fetur.
A ranar 16 ga Maris, 2025 kwamitin ya sanar da ƙwato kuɗaɗen da suka sauya sheka daga kamfanonin mai kimanin Naira biliyan 28.7 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 19.24, wanda ya kawo jimillar kuɗazen da aka kwato zuwa dala miliyan 33.44 (kimanin miliyan N50.1).
Taƙaddamar da aka samu na baya-bayan nan ya nuna cewa daga man fetur, an samu dala miliyan 1.9 (biliyan N2.9), yayin da aka ƙwato dala miliyan 1.578 (biliyan N2.3 daga mai da iskar gas).
A wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar, Akin Rotimi, ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, ta ruwaito shugaban kwamitin, Bamidele Salam, yana bayyana nasarorin da aka samu ga goyon baya da jagorancin kakakin majalisar Tajudeen Abbas.
A cewarsa, tsayuwar dakan da kakakin majalisar ya yi na sa ido da kuma bin doka da oda, ya tabbatar da cewa kwamitoci suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, ba tare da tsangwama ba, tare da bayyana hurumin kare dukiyar al’umma.
