An yi bikin naɗin sarautar Akeem Owoade a matsayin Alaafin na Oyo na 46

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Asabar ne aka naɗa Oba Akeem Owoade a matsayin sabon Alaafin na Masarautar Oyo, wanda kuma shi ne na 46 daga cikin waɗanda suka taɓa riƙe muƙamin.

Ya gaji Oba Lamidi Adeyemi ne a kujerar, wanda ya rasu a watan Afrilun 2022 bayan ya rayu da shekaru 83 a duniya.

An gudanar da taron naɗa shi ne a makarantar Oliveth Baptist High School a Oyo, inda Gwamna Sayi Makinde ya jagoranci sauran masu alfarma da suka halarci taron.

Ga jaddawalin waɗanda suka halarci taron kamar yadda jaridar ‘Intelregion’ ta ruwaito: “Olubadan of Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin; the Ooni of Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi; the Soun of Ogbomoso, Oba Ghandi Olaoye; Oluwo of Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi; and Aare Oona Kankanfo of Yoruba, Iba Gani Adams.”

Sauran sun haɗa da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar; “Aare Musulumi of Yorubaland, Alhaji Dahud Makanjuola; Bishop Taiwo Adelakun; former MILAD, General Adebayo Popoola; Aseyin of Iseyin Oba Sefiu Oyebola; Olu of Igboora, Oba Jimoh Titiloye and Asigangan of Igangan, Oba Rafiu Ariwoola among others.”

Hakan ya biyo bayan cike sharuɗɗan wasu al’adun gargajiya da na Gwamantin Jihar Oyo da Oba Owoade ya yi, wanda ya kammala a ranar 21 ga watan Maris, 2025.

By Babaji