
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Ilimi, Olatunji Alausa ya yi kira da ƙara wa’adin hidimar ɗaliban NYSC daga shekara ɗaya zuwa biyu.
Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a lokacin da Darakta-Janar na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Nafiu ya ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja.
Ya ce, za a yi hakan ne yayin da aka faɗaɗa ayyukan koyar da sana’o’i a tsarin hidimar ɗaliban, wanda yin hakan zai bada dama a gare su ta dogaro da kawunansu a yayin da suka kammala.
Ya kuma yi kira da a kara adadin ƴan NYSC da ake tura wa makarantu a ƙauyuka, wanda hakan zai taimaka wajen cike giɓin malamai da ake samu a lokuta da dama.
A nasa jawabin, Shugaban NYSC B.J. Nafiu, ya yi kira da a samar da tsarin tattara bayanan baki ɗaya ɗaliban da ke karatu a ƙasashen waje, wanda ya ce zai taimaka wajen sauƙaƙe wa gwamnati da sauran masu-ruwa-da-tsaki kan harkar ilimi fitar da ingantattun bayanai da yaƙar amfani da takardun kammala karatu na bogi.
Ministan ya ce tuni suka fara ƙoƙarin hakan tare da tabbatar masa da cewa za su ƙarfafa alaƙoƙi tsakanin Ma’aikatar da NYSC don warware matsalolin da ake fuskanta da kuma inganta harkokinsu.
