‘Yan sanda sun janye gayyatar da suka yi wa Sarki Sanusi

Spread the love

Rundunar ƴan sanda ta ce ta janye gayyatar da ta yi wa Sarki Muhammadu Sanusi na II, bisa wata hatsaniya da ta faru a ranar Idin Ƙaramar Sallah.

A kwanakin da suka gabata ne rundunar ta gayyaci sarkin domin bayar da bahasi akan abinda ya faru a ranar Idin a lokacin da sarkin ke komawa gida akan doki bayan kammala sallar Idi, inda wasu matasa suka far wa tawagarsa har suka halaka ɗaya daga cikin masu ba shi kariya..

To sai dai cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce ta janye gayyatar bisa shawarar wasu mutane da ƴan sandan suka kira ”masu ruwa da tsaki da take kimantawa”.

Haka kuma ƴan sandan sun ce daga cikin dalilan janye gayyatar har da muradin babban Sufetonsu na tabbatar da cewa ba a siyasantar da aikin ƴan sanda ba ko yi wa aikin mummunar fahimta.

”A maimakon haka babban sufeton ƴan sandan ya aike da wata tawagar rundunar ta sashen tattara bayanan sirri da su je fadar sarkin domin jin bahasinsa kan abin da ya farun”, in ji sanarwar.

Gabanin bukukuwan ƙaramar sallah ne dai rundunar reshen Jihar Kano ta fitar da sanarwar hana Hawan Salla, saboda bayanan da ta ce ta samu na sirri da ke nuna cewa za a iya samun rikici.

By Babaji