“Burina na cigaba da bayar da gudunmawa ga adabin Hausa, ta hanyar rubutu da wallafa”
(Ci gaba daga makon jiya)
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A makon da ta gabata, mun ɗauko tattaunawa da haziƙin marubuci da ya jima yana bada gudunmawa a harkar Adabin Hausa, wato ɗanladi Z. Haruna, inda muka kwana a tambayar da muka yi masa na ko an taɓa damfararshi ta hanyar fasahar zamani da ya ja hankalinsa ga rubuta littafi kan hakan. Tambayar wadda marubucin bai kai ga bada amsa ba muka dakata tare da alƙawarin waiwayar ta kafin wasu tambayoyin da za su biyo baya.
Kamar dai wancan satin, wakilinmu a Jos ne ya jagoranci tattaunawar. A sha karatu lafiya:
MANHAJA: Shin an taɓa damfararka ko cutar da kai ta hanyar fasahar zamani, da ya ja hankalinka wajen rubuta littafin ‘ɓarayin Zamani’?
ɗANLADI: Wannan tambaya na da muhimmanci ƙwarai. A 2009 ina hidimar ƙasa a Jihar Osun. Na je wani banki na saka katina na ciri kuɗi. Da yake da jama’a a bayana ina sauri na bar wurin. Kuɗin na fitowa na yi gaba ban ɗauki katin nawa ba. Har na yi nisa aka ƙwala min kira na koma na ga ashe ma na manta katin a jikin injin. Sai da na koma masauki na lura ashe ba katin nawa ba ne tuni an sauya min da wani irinsa. A lokacin ban damu sosai ba domin a zatona tunda ba su san kalaman sirrina ba, ba za su iya komai ba. Kuma ma zan iya zuwa a sauya mini wani katin. To, amma cikin daren wannan ranar na yi ta ganin saƙonni na fitar kuɗi har sai da aka tatike asusun nan bakiɗaya. Washegari na ruga banki suka ɗan yi nasu binciken ba a iya gano yadda ma aka sace kuɗin ba. Da wannan na soma nazari da bincike kan yadda ake iya satarwa mutum kuɗi daga banki ba tare da ya aminta ba. Haka dai na yi ta bincikawa har yanzu ma da sababbin dabaru ke sake bayyana. Wataƙila nan gaba na sake rubuta wani littafin makamancin ‘ɓarayin Zamani’ wanda ke magana akan sabbin dabarun laifuffukan intanet da hanyoyin kare kai.
Yaya kake kallon muhimmancin irin waɗannan rubuce-rubuce wajen ilimantar da masu karatu game da matsalolin da ke damun su?
Rubuce-rubuce kamar irin littafin ‘ɓarayin Zamani’ na da matuƙar muhimmanci wajen wayar da kai, domin suna bayani kan matsalolin zamantakewa da hanyoyin magance su. Suna ilimantar da masu karatu ta hanyar labarai masu jan hankali, suna ƙarfafa tunani mai zurfi da faɗakarwa. Haka kuma, suna taimaka wa wajen gyaran tarbiyya da hana aikata munanan ayyuka a cikin al’umma.
Wacce gudunmawa Gasar Tsangayar Gusau ke bayarwa wajen ƙyanƙyashe jajirtattun marubuta adabin Hausa?
Gasar Tsangayar Gusau na taka muhimmiyar rawa wajen ƙyanƙyashe jajirtattun marubuta adabin Hausa ta hanyar ba su bigire na musamman da suke nuna hazaƙarsu. Gasar tana ƙarfafa gwiwar marubuta, musamman matasa, don su rungumi rubuce-rubuce da kyakkyawan tsari. Ta hanyar ba da horo, shawarwari, da kyaututtuka, gasar na taimakawa marubuta su inganta fasaharsu, kuma tana ƙara martaba ga adabin Hausa.
Bugu da ƙari, gasar na ƙarfafa ƙirƙira da sabbin dabaru a cikin adabi, tana samar da marubuta masu himma da za su ci gaba da raya harshen Hausa. Haka nan, tana taimaka wa wajen haɓaka sha’awar karatu da rubutu, musamman ga matasan da ke sha’awar rubuce-rubuce. Gudunmawar gasar na tabbatar da ɗorewar adabin Hausa da kuma ɗaukaka al’adu da tarihin Hausawa ta hanyar rubuce-rubuce masu ma’ana da fa’ida.
Ka ga dai yanzu abu ne mai wahala marubuci ya iya wallafa littafi saboda dalilai da dama da suka haɗa da hauhawar farashi da rashin son karatu sosai, amma ita Cibiyar Gusau na taka rawa muhimmiya wajen wallafawa marubuta littatafansu ga kuma tallafin kuɗi da yayata marubuci a idon duniya. A sanina dai, wannan gasar ce kurum ake ɗaukar nauyin buga littafi sukutum na marubucin Hausa. Muna fatan Allah ya ƙarfafe su su cigaba da wannan namijin ƙoƙari har zuwa bayyanar Mahadi.
Shin har yanzu kana da burin cigaba da rubutun adabi?
Wuuu, ai rubutu a cikin raina yake, yana gudana cikin jikina a yau da gobe. Kusan kullum a cikinsa nake, domin rubutu wani ɓangare ne na rayuwata da ba zan iya rabuwa da shi ba. Babu ranar da ba na rubutu—ko dai ƙirƙirar ƙagaggun labarai, nazari, ko kuma irin na makaranta wato ‘Academic Writing’.
Burina bai taɓa gushewa ba, sai ma ƙara ƙarfafa. Ina da shirin cigaba da rubuce-rubuce masu ma’ana da fa’ida, don ƙarfafa al’adunmu da harshenmu. Sai dai babban ƙalubale shi ne wallafa littattafai, wanda ke buƙatar kuɗaɗe, lokaci, da ƙoƙari mai yawa. Amma duk da haka, burina shi ne na cigaba da bayar da gudunmawa ga adabin Hausa, ta hanyar rubuce-rubuce da wallafa ayyuka da za su taimaka wa al’umma, musamman matasa masu sha’awar karatu da rubutu.
Yaya ka ji lokacin da ka samu nasara a Gasar Marubuta ta Gajeren Labari da Hukumar Tace Finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano ta shirya a shekarar da ta gabata?
Watau kamar kowacce gasa, haƙiƙa na ji farin ciki sosai da nasara a Gasar Marubuta ta Gajeren Labari da Hukumar Tace Finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano ta shirya, domin ta nuna cewa ƙoƙarina na rubutu yana samun karɓuwa. Wannan nasara ta ƙarfafa ni don cigaba da inganta ƙwarewa, ta ba ni damar haɗuwa da sauran marubuta, da kuma ƙarfafa imanina cewa zan iya cimma burina. Haka nan, ta ƙarfafa al’adar karatu da rubutu a cikin al’umma, musamman a tsakanin matasa. Wannan babbar daraja ce a gare ni, kuma tana ƙara min kwarin gwiwa wajen wallafa littattafai.
Har ila yau ta sa na sake amanna da jagorancin wannan hukuma yadda a halin yanzu suke jan marubuta a jiki. Kafin a zo ga wannan mataki, an sha jidali da faɗi tashi da ɗauki ba daɗi tsakanin marubuta da jagororin hukumar a zamanin baya. Iyayen gidanmu marubuta da manazarta sun sha fama ƙwarai da gaske irin yadda hukumar a baya ta yi musu fyaɗar ‘ya’yan kaɗanya tare aibata su da muzanta da shafa musu kashin kaji. Yanzu kuwa marubuta sun zama sha lele, ‘yan gata kuma zaɓaɓɓu da ake damawa da su cikin wannan hukumar. Wannan kam ba ƙaramar nasara ba ce. Muna godiya ga iyayen gidanmu marubuta da suka yi tsayuwar daka wajen tabbatar da wannan haɗaka. Muna fatan kuma ba za mu ba su kunya ba a yanzu da gobe da an jima.
Da wanne labari ka samu nasara kuma wanne saƙo yake isarwa?
Da farko dai gasar an gina ta ne akan tambihi kan kyawawan al’adun Hausawa na gargajiya da kuma irin tasirin su a zamantakewar yau da kullum. Don haka na gina labarina mai taken ‘Gadon Gida Sai da Horo’ ne bisa doron buƙatar wannan gasa.
Labarin ya mayar da hankali ne kan muhimmancin haƙuri, ƙoƙari, da rungumar gadon al’adu da sana’o’in gida wajen cimma nasara. Yana bayyana yadda son hanzarta samun nasara ba tare da aiki ba ke jefa mutum cikin matsala.
Inuwa, jarumin labarin, ya guji gadon iyayensa na noman gargajiya da kiwo da kuma laftun jakai. Burinsa kurum ya samu kuɗi ko dukiya ta hanya mafi sauƙi. Don haka yake ta karakaina tsakanin ƙarya da gaskiya da neman jalabi daga ‘yan tsibbu. Sai dai duk abin da ya sa hannu sai ya zama tamkar tafiyar kura watau idan an yi gaba sai a yi baya. ƙarshe dai ya tari aradu da ka ya shiga wasan dambe wanda bayan sa toka sa katsi aka rafke shi bai tsinci kansa ba sai a gadon asibiti.
Ta hanyar rarrashi da nuni da nasiha mahaifinsa ya jawo hankalinsa kan komawa sana’ar gida wadda ke koyar da juriya, haƙuri, da kuma jajircewa. Inuwa ya gane cewa ashe kowa ya bar gida, gida ya bar shi. Ya naƙalci cewa hatta gadon gidan nasu ma da ya raina ba zai iya tsinana komai ba sai an ba shi horo. Kenan ba gaskiya ba ne da ake cewa gado kaɗai ya isa mutum ya shahara koda bai yi aiki tuƙuru ba.
Wannan labari yana da nufin jan hankalin matasa su fahimci cewa nasara tana buƙatar haƙuri, nutsuwa, da kuma rungumar abubuwan da ke kusa da su. An yi amfani da kalmomi da muhallin gargajiya sosai domin neman dacewa da abin da gasar ta ƙunsa.
Wanne buri ka ke da shi na ganin an ƙara bunƙasa harkar rubutun adabi?
Burina shi ne ganin an ƙara bunƙasa harkar rubutun adabi ta hanyar ƙarfafawa marubuta, haɓaka ingancin rubuce-rubuce, da kuma ba da damar yaɗuwar ayyukan adabi a cikin al’umma. Ina fatan an ƙara tallafa wa marubuta, a ƙara samun damarmakin bincike da haɓaka al’adun rubutu, kuma a ƙara wayar da kan jama’a game da muhimmancin adabi wajen cigaban al’umma.
A wani lokaci a can baya, akwai wani yunƙuri da aka ce kun fara don samar da wata sabuwar hanyar taskance littattafan Hausa a manhajar zamani, a ina aka kwana?
Ana ta faɗi tashi akan wannan. Ina cikin shirye-shirye da dama da wasu ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni ke yi na taskace ayyukan adabi a hanyoyin zamani na dijital. Sai dai har yanzu wannan yunƙuri bai kai ga bugun ƙirji a samu wani abin kai wa ga baka ba. Amma tabbas idan an cigaba yadda aka fara ɗin nan, babu jimawa kwalliya za ta biya kuɗin sabulu. Akwai ayyukan da muke sa ran za su fito a wannan shekara ta 2025 cikin irin yunƙurin da ake yi.
Kana ganin nan gaba za a iya dawo da buga littattafan Hausa kamar yadda ake yi a baya?
Dawo da buga littattafan Hausa kamar yadda aka yi a baya abu ne mai kamar wuya, saboda sauye-sauyen da aka samu na halayyar masu karatu, da rashin wadataccen kuɗin ɗab’i, da tasirin fasahar dijital da rashin hanyoyin rarraba littatafan kamar a baya da dai sauransu. Yanzu mutane sun fi karkata ga e-books da audiobooks, kuma rashin cibiyoyin rarrabawa da masu siyarwa ya sa kasuwar littattafan Hausa ke ƙara raguwa. Bugu da ƙari, rashin tallafi daga gwamnati da masu zaman kansu ya sa marubuta da gidajen buga littattafai suka fuskanci ƙalubale wajen ci gaba da wallafa ayyukansu.
Duk da haka, akwai hanyoyin da za a iya bi don farfaɗo da littattafan Hausa. Ana iya amfani da fasahar dijital domin yaɗa littattafan Hausa a dandamali na zamani, tare da haɗa su cikin manhajojin karatu. Haka nan, tallafi daga gwamnati, cibiyoyin al’adu, da kamfanonin buga zai taimaka wajen rage tsadar wallafawa. Shirya tarukan karatu, tallata littattafai ta shafukan sada zumunta, da ƙarfafa gidajen buga littattafai na gida zai iya taimakawa wajen farfaɗo da wannan al’ada. Sannan kuma, ya kamata a riƙa duba littatafai masu amfani ana saka su a cikin manhajar makarantu ta yadda za a samu cusawa ɗalibai kishin karatu da nazari.
To ka ga, kodayake dawo da buga littattafan Hausa kamar yadda ake yi a baya yana da wahala, akwai hanyoyin da za a iya bi wajen ƙoƙarin farfaɗo da rubuce-rubuce masu amfani waɗanda za su iya taimaka wa wajen farfaɗo da kasuwancin littattafan Hausa.
Ta yaya za a inganta kasuwancin littattafan Hausa ta hanyar zamani?
Za mu ci gaba a mako mai zuwa. Inda da yardar mai dukka za mu kawo ƙarshen tattaunawar, kafin wasu tambayoyin za mu soma da wadda muka dasa aya da ita.
