Aƙalla matafiya bakwai ne suka rasa rayukansu bayan wani fashewar bama-bamai a kan titin Maiduguri-Damboa da ke jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa bam ɗin ya fashe ne a lokacin da wasu jerin gwanon motocin fasinja da ke ƙarƙashin rakiyar dakarun soja ke tafiya daga Damboa zuwa Maiduguri, a ranar Asabar. Lamarin ya auku ne a wani sashe na hanyar da ke cikin dajin Sambisa, inda ‘yan Boko Haram ke kai hare-hare.
Wannan hanya tana da matukar muhimmanci wajen haɗa Maiduguri da ƙananan hukumomi da dama a Kudancin Borno, amma ta daɗe tana rufe sakamakon hare-haren da ‘yan ta’addan ke kai wa. Gwamnatin Babagana Umara Zulum ce ta sake buɗe hanyar, inda ake tafiye-tafiye ne sau biyu a mako ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro da rakiyar sojoji.
Wani ganau ya bayyana cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti a Maiduguri domin samun kulawar gaggawa. Har yanzu ba a bayyana adadin cikakkun waɗanda suka jikkata ba.
