Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Alamu sun nuna cewa ’yan Nijeriya za su samu ragin kuɗin sayen man fetur kamar yadda farashin ɗanyen mai na Brent ya ragu zuwa dala 65 kan kowacce ganga daga dala 69.90 a kasuwannin duniya.
Ana amfani da farashin Brent a duk duniya don daidaita farashin sauran ɗanyen mai – manyan kayan abinci – da kuma ƙarin farashin kayayyakin man fetur.
Farashin ɗanyen mai na Brent, ma’aunin mai a duniya, ya ragu da kashi 7 bisa ɗari zuwa ciniki a kan dala 65.58 – mafi ƙanƙanta tun Afrilu 2021.
Amurka West Teɗas Intermediate (WTI) kuma ta ragu da kashi 7.35 zuwa 62.03 kan kowace ganga.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, farashin ɗanyen mai ya faɗi a yayin da ƙasar Sin ta ƙara haraji kan kayayyakin Amurka a wani mataki na ramuwar gayya, lamarin da ya kara zafafa yakin cinikayya a duniya, wanda ya sanya masu zuba jari suka damu da koma bayan tattalin arziki.
A ranar 2 ga Afrilu, Shugaba Donald Trump ya ba da sanarwar tsawaita haraji a duk duniya kan duk wasu kayayyaki da ake shigowa da su Amurka, wanda ya sanya kashi 14 cikin 100 kan Nijeriya.
Kwana guda bayan haka, Ngozi Okonjo-Iweala, Darekta-Janar na ƙungiyar Ciniki ta Duniya WTO, ta ce harajin da Amurka ta bayyana na baya-bayan nan zai yi matuƙar tasiri ga harkokin kasuwanci da ci gaban tattalin arzikin duniya.
Tuni dai farashin sarin mai na Mainland, A.Y.M da kuma Eɓer ya ragu zuwa N918 a kowace lita daga N920 da kuma N919 daga N920 kan kowace lita.
Haka kuma, farashin sari na Prudent, Eterna da Soroman ya ragu zuwa N912 daga N913 kowace lita, N897 daga N900 a kowace lita, N915 daga N916 kowace lita.
A cewar petroleumprice.ng, masu sayar da mai za su iya daidaita farashin lita zuwa ƙasa yayin da suke samun sabbin kayayyaki a mako mai zuwa, idan yanayin kasuwan ya ci gaba.
