
Daga BELLO A. BABAJI
Wani ɗalibin Jami’ar Awolowo, Ile Ife a Jihar Osun, ya rasa ransa a yayin ɗauko ƙwallon ƙafa a wani gida a yankin Moro, sakamakon haɗuwa da wayar wutar lantarki.
Wani shaida ya ce, lamarin ya auku ne a lokacin da suke tsaka da wasa, inda mamacin ya buga ta cikin wani gida. Ganin haka ya sa ya haura katangar gidan da nufin ɗauko ta.
Bayan ya ɗauko ƙwallon tare da jefa wa abokan wasansa ne, sai ya nufi sake haura katangar don fitowa daga gidan, inda a nan ya haɗu wayar lantarkin.
Kakakin Jami’ar, Abiodun Olanrewaju ya tabbatar da faruwar al’amarin tare da miƙa saƙon jaje ga iyalan ɗalibin.
Ya ce, duk da cewa sauran ɗaliban sun yi ƙoƙarin ɓare shi da sanda daga wayar, an tabbatar da mutuwarsa a yayin da aka garzaya da shi asibiti.
Saidai, har zuwa lokacin kammala haɗa rahoton ba a bayyana sunan ɗalibin ba duk da cewa wasu daga cikin wakilan Jami’ar sun ziyarci gidansu, kamar yadda Kakakin ya bayyana.
