Cibiyar ‘yan jarida ta duniya (IPI) reshen Najeriya ta sanar da naɗin wasu fitattun ’yan jarida da jami’an gwamnati cikin kwamitocinta domin inganta ’yancin fadar albarkacin baki da kuma aikin jarida mai inganci a ƙasar. Cikin kwamitocin akwai waɗanda ke kula da tara kuɗaɗe, shirye-shirye, fafutuka da kuma membobinsu, inda aka haɗa su da ƙwararru daga ɓangarori daban-daban na kafafen yaɗa labarai.
Daga cikin waɗanda aka naɗa akwai ministan watsa labarai da wayar da kan jama’a, Alhaji Mohammed Idris; tsohon mai magana da yawun tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu; tsohuwar shugabar ƙungiyar Editocin Najeriya (NGE), Mrs. Funke Egbemode; da kuma tsohon shugaban makarantar koyar da aikin jarida ta ƙasa, Mr Gbemiga Ogunleye. Mrs. Egbemode za ta jagoranci kwamitin tara kuɗaɗe, yayin da sauran fitattun ’yan jarida da masana za su riƙe manyan muƙamai a sauran kwamitoci.
Shugaban IPI Nigeria, Musikilu Mojeed, ya ce sake fasalin waɗannan kwamitoci na da nufin ƙara azama wajen kare ’yancin kafafen yaɗa labarai da kuma tabbatar da ayyukan jarida masu inganci a Najeriya. Kwamitocin za su aiwatar da dabarun jawo sabbin mambobi, shirya muhimman ayyuka, da kuma tunkarar batutuwan da suka shafi ’yancin jarida a matakin ƙasa da ƙasa.
