
Daga BELLO A. BABAJI
Babbar jam’iyyar adawa, PDP, ta sanar da ƙin amincewarta ga shirin haɗaka tsakanin jam’iyyun siyasa domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Wannan ɗaya ne daga cikin ababen da aka cimma a yayin zaman gwamnonin jam’iyyar da ya gudana a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, tsakanin ranakun Lahadi da Litinin.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin kuma Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya bayyana hakan jim-kaɗan bayan kammala zaman ga manema labarai.
Ya ce, suna maraba ga dukkan wani ko wasu da ke da ƙudirin shiga jam’iyyar.
An gudanar da zaman ne ba tare da dakataccen Gwamnan Jihar Ribas ba, wato Siminalayi Fubara. Haka ma Jami’yyar SDP ta ƙi amincewa da batun haɗakar.
Ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP, Alhaji Atiku Abubakar da takwaransa na Jam’iyyar LP, Peter Obi sun haɗu akan kira ga samar da jam’iyyar haɗaka da za ta kayar da APC a 2027.
