
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon mataimaki ga tsohon Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, Kwamared Anas Abdullahi Ƙaura, ya zargi Gwamnan jihar na yanzu, Dauda Lawal da bada bayanan ƙarya game da asusun gwamantin jihar don ɓata wa Matawalle suna.
Ya yi ikirarin cewa, Matawalle ya bar sama Naira biliyan 25.9 a asusun a lokacin da ya miƙa mulki ga Lawal a watan Mayu, 2023.
A wata takarda da ya fitar a Abuja, Ƙaura, wanda ya kasance mai bai wa tsohon gwamnan shawara kan harkokin birane da tsare-tsaren shiyyoyi, ya bayyana Gwamna Dauda Lawal a matsayin maƙaryaci bayan ya zargi tsohuwar gwamnatin da barin asusun gwamantin babu komai.
Ya ce, lallai an bar kuɗaɗe tare da takardun bayanai akan su, ya na mai ƙalubalantar sa da ya tabbatar da akasin haka don kare abinda ya faɗa.
A ranar Lahadi ne yayin hira da gidan talabijin na ‘Arise’, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, Naira miliyan huɗu kacal ya gada daga gwamantin baya tare da bashi mai tarin yawa.
Ya kuma ce, ya samu jihar a mawuyacin hali, inda kowane ɓangare na fuskantar tsaiko da barazanar taɓarɓarewar al’amura.
Saidai, Kwamared Ƙaura ya musanta batun da cewa gwamnan ya yi hakan ne don neman ɓata sunan Matawalle, alhalin biliyoyin kuɗaɗe ya gada.
Har’ilayau, ya caccaki gwamnan da yawan tafiye-tafiye a madadin ƙaddamar da ayyuka kamar yadda takwarorinsa na Kaduna da Sakkwato ke yi, yayin da al’ummarsa ke fama da matsanancin tsaro da yunwa.
