NULGE ta yi kira ga shugabannin ƙananan hukumomi a Katsina da su mai da hankali wajen kulawa da ma’aikata

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta ƙasa reshen Jihar Katsina Kwamared Nasiru Wada Mai’adua ya yi wannan kira da yake hira da manema labarai a Katsina.

Ya ce ƙungiyar sa zata ba shugabannin cikakken goyon baya wajen samar da ababen more rayuwa musamman a yankuna karkara.

Kwamred Nasiru Wada ya kuma taya sabbin shugabannin murnan kama aiki a matsayin jagororin ƙananan hukumomi 34 da ke jihar.

“Tun da za a sakan maku kuɗaɗen ƙananan hukumomi babu dalilin da zai sa ba zaku kawo cigaba a yankunan ba tare da canza rayuwar al’ummar karkara”shugaban NULGE ya ce.

Ya kuma yi kira a garesu da su bada fifiko kan samar wa ma’aikatan ƙananan hukumomi samun horo sau biyu ko uku a shekara domin ƙara samun ƙwarewa na tafiyar da harkokin aikin su dai zai daidai da zamani.

Haka kuma ya jawo hankalin shugabannin ƙananan hukumomin da su tabbatar da biyan duk hakkokin ma’aikata domin samun nasarar aiwatar da manufofin su na inganta rayuwar al’umma.

Ya kuma jawo hankalin ya’yan ƙungiyar da su ba shugabannin ƙananan hukumomin cikakken goyon baya da zuwa wajen aiki akan lokaci da nuna biyayya ga hukumomi.

Kwamred Nasiru Wada ya kuma yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa kan samun nasarar samar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomin bayan kammala zaɓen su daya gudana watanni kusan uku da suka wuce.

By ukarofi