Daga JAMEEL GULMA a kebbi
Rahotanni daga ƙaramar Hukumar mulki ta Argungu sun bayyana cewa bayan tayar da jijiyoyin wuya na wani lokaci kansilolin ƙaramar hukumar mulkin sun tsige kakakinsu, Honarabul Zayyan Alhassan, kansila mai wakiltar mazaɓar Lailaba kuma nan take suka maye gurbinsa da Honarabul Mukhtar Umar Gero daga mazaɓar Gwazange a matsayin sabon jagoran kansilolin.
Wannan ya biyo bayan wani zama da suka gudanar ranar Laraba 16 ga Afrilu, 2025 inda bayan zaman suka fitar da wata takarda mai ɗauke da sa hannun kansilolin da ta ke bayyana tsige Muhammed Zayyan tare da maye gurbinsa da Honarabul Muktar Umar Gero.
Takardar ta bayyana dalilan tsige Muhammed Zayyan sun haɗa da yaudara da rashin ɗaukar shawara da cin amanar abokan aiki da yin gaban kan sa ba tare da tuntuɓa ba.
Wannan shi ne karo na biyu da Honarabul Muktar Umar Gero ya zama shugaban kansilolin ƙaramar hukumar mulki ta Argungu a ƙasa da watanni bakwai wanda an taɓa tsige shi bayan wani kai ruwa rana tsakanin sa da ɗaya daga cikin kansilolin a ‘yan watannin baya.
Bayan tsige tsohon shugaban kansilolin da kuma naɗa sabon an yi sauye-sauyen mukamai a jagorancin kansilolin da suka hada da Honarabul Zayyanu Muhammad Musa daga mazaɓar Dilko a matsayin mataimakin shugaba (Deputy Council Leader) sai Honarabul Bahari Usman daga mazaɓar Zazzagawa a matsayin mai tsawatarwa (Chief Whip).
Sai kuma Honarabul Shafi’u Sani Umara daga mazaɓar Alwasa/Gotomo a matsayin Jami’in hulɗa da jama’a (PRO).
Bayanai da wakilinmu ya tattara sun nuna wannan rikicin ya samo asali ne sanadiyyar bambance-bambancen iyayen gida a siyasance ne ke ruruta wuta a tsakanin kansilolin duk da kasancewarsu ‘ya’yan Jam’iyyar APC ne da ke mulki a jihar.
ɗaya daga cikin kansilolin ya bayyanawa wakilinmu da cewa, “babbar matsalar da ke kawo wannan sauye-sauyen shi ne akwai son girma don kashi biyu daga cikin uku suna da ra’ayin son a girmama su, akwai kuma yawo da kananan maganganu suna kushe junan su saboda neman a yaba musu, akwai kuma rashin amana musamman a wajen aiwatarda ayukan su suna wuce iyaka saboda sai da yawa idan aka zauna aka zartar da wani al’amari sai ka ga ana tinkarar manya ba bisa ladabi ba wanda a karshe duk mai hankali ya kan kalli yin haka a matsayin cin zarafin shugaba ne.”
Ya ƙara da cewa, “gyaran ire-iren waɗannan matsalolin yana da wahalar gaske saboda siyasar ta kasu zuwa gidaje daban-daban wanda kuma su shugabnnin shirinsu yana wuyar gaske amma tun da ya ke abin ya zama haka idan su shugabannin sun gagara haɗuwa to mu da mu ke yaran su a duk lokacin da za mu gaya musu magana to mu je musu da maganar gaskiya ba sukar juna ba wanda ko kaɗan ba ya kawo alheri. In Sha Allahu idan ƙananan za su zo wa manya da maganun gaskiya wata rana su da kan su za su yi wa kawunan su kiyamul-laili.
“Shi kuma wannan sabon shugaban da ya dawo Honarabul Muktar Umar Gero ba shakka shugaba ne saboda duk kansilolin sun tabbatar da ba ya munafurtar kowa amma yana da rauni na ɗaukar matakin magance matsala da wuri.
“Alhamdu lillahi yanzu dai an yi walkiya an ga kowa a fili saboda an ga takon Muktar Gero an kuma ga ta Alhassan wanda bai wuce ‘yan kwanaki kaɗan da ɗorawa ba ya rinƙa cin zarafin shugaba da abokan aikin sa ballantana sauran mutane wanda tun nan kai tsaye kansiloli takwas daga cikin goma sha ɗaya suka lamunce da a mayar da Muktar Umar Gero,” inji shi.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin tsigaggen shugaban kansilolin Honarabul Zayyan Alhassan inda ya ce ba wata matsala tsakaninsa da abokan aikinsa illa dai an ba shi shugabanci ne kuma an tsige shi, shi kuma shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Argungu Honarabul Aliyu Sani Gulma bai ɗauki waya ko mayar da amsar saƙon kar ta kwana ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
Siyasar Argungu dai ta daɗe tana fama da wannan rarrabuwar kai saboda bambancin uwayen gidan siyasa dake addabarsu, inda gidajen sun haɗa da ɓangaren tsohon mataimakin gwamnan jihar Kebbi kuma tsohon ɗan majalisar wakilai Honarabul Bello Dantani da ɓangaren Sakataren tsare-tsare na Jam’iyyar APC ta ƙasa kuma tsohon mataimakin gwamnan Kebbi Alhaji Sulaiman Muhammad Argungu (Jarman Kabi) da kuma ɓangaren Mataimakin gwamnan jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar Argungu (Tafidan Kabi) sai kuma ɓangaren tsohon ɗan majalisar wakilai Honarabul Bashar Matawalle da shugaban Jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar mulki ta Argungu Alhaji Aliyu Abdullahi (Hard game)
Waɗannan ɓangarorin sun daɗe suna yi wa juna kallon hadarin kaji da suna iya duk yadda za su yi don cimma biyan buƙatarsu a kan abokan hamayyar cikin gida duk da kasancewarsu ‘ya’yan Jam’iyyar APC ne a yanzu da ba wani bambancin siyasa.
