Boko Haram ta kashe mutum bakwai a Adamawa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Aƙalla mutane bakwai ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani ƙazamin hari da ’yan Boko Haram suka kai a ƙauyen Garaha Lar da ke jihar Adamawa.

Shugaban ƙaramar Hukumar Hong, Usman Wa’aganda, wanda ya tabbatar da harin, ya ce wani mazaunin garin ya ɓata yayin da maharan suka lalata gidaje da kadarori.

Wa’aganda ya kuma bayyana cewa, wani ɗan sintiri na yankin ya mutu bayan da wani bom ya tashi a lokacin da yake ƙoƙarin kare yankin.

Ya ce, motar ’yan sandan da ke sintiri daga ofishin ‘yan sanda na Garaha ita ma an lalata da bom da aka dasa, amma babu wani mutum da ya mutu.

“Mutane da ke cikin motar sintirin sun fito daga cikin motar kafin fashewar,” inji shi.

Shugaban ya ce, tsoron bama-baman da maharan suka dasa ya sanya shiga wurin da aka kai harin ke da wuya.

Sai dai ya roƙi a tura sojoji yankin da matsuguni ga waɗanda abin ya shafa.

“Kamar yadda nake magana da ku a yanzu, mutane da yawa ba su koma gida ba, kuma ba a samun inda aka kai harin saboda fargabar bama-bamai da maharan suka dasa,” inji shi.

“Muna roƙon a kara tura sojoji da kuma kai ɗauki ga waɗanda abin ya shafa,” inji shi.

By ukarofi