GenCos sun yi barazanar jefa Nijeriya a duhu kan bashin tiriliyan N4

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Matsalar lantarki na iya sake ƙara kunno kai a daidai lokacin da ƙungiyar Kamfanonin Samar da Wutar Lantarki (APGC) ta yi gargaɗin rufe ayyuka a Nijeriya, tare da yin Allah wadai da ɗimbin basussukan da ta ke bin Gwamnatin Tarayya.

Sani Bello, shugaban kwamitin amintattu na APGC, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Litinin, inda ya bayyana cewa rashin samun kuɗi a masana’antar samar da wutar lantarki na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke hana ‘yan Nijeriya ci gaba da samun tsayayyen wutar lantarki.

Ya yi nuni da cewa kamfanonin da ke samar da wutar lantarki (GenCos) sun ci gaba da ɗaukar nauyin matsalar ƙarancin wutar lantarki a masana’antar samar da wutar lantarki ta Nijeriya (NESI), alhali ba laifin su ba ne.

A cewarsa, a halin yanzu GenCos na bin bashin kusan Naira Tiriliyan 4 (tiriliyan N2 na 2024 da kuma Naira Tiriliyan 1.9 na basussukan baya) ba tare da wata hanyar da za ta iya magance su ba, da suka haɗa da biyan kuɗi, kayan aiki da musanya basussuka.

Ya ci gaba da cewa, kasafin kuɗin gwamnati na 2025 na ware Naira biliyan 900 ne kacal ga wutar lantarki, wanda hakan ya haifar da damuwa game biyan basussukan da ake bin gwamnatin da kuma biyan bashin nan gaba.

By ukarofi