‘Yan bijilante 15 sun rasu a yayin harin sabuwar ƙungiyar ta’addanci ta ‘Mahmuda’ a Arewa ta Tsakiya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kimanin ƴan bijilante 15 ne suka rasa rayukansu a yayin harin wasu ƴan ta’adda a wasu yankunan Arewa ta Tsakiyan Nijeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa, maharan sun bayyana ne daga wata sabuwar ƙungiya da aka yi wa laƙabi da ‘Mahmuda’, wadda ke kai farmaki a garuruwan da ke kusa da tafkin Kainji, wato Kainji Lake National Park.

Yankin, waje ne da ke kan iyakar Jihohin Neja da kwara wanda ya haɗa ƙauyuka da dama na ƙananan hukumomin jihohin.

Wasu daga cikin yankunan a Ƙaramar Hukumar Kaiama sun haɗa da Kemaanji, Tenebo, Baabete, Nuku da Nanu; sai kuma Ƙaramar Hukumar Barutein a wasu ƙauyuka dake Gundumar Yashikira duk a jihar Kwara.

Haka kuma, ƙungiyar ta karɓe iko da wasu ƙauyuka a Gundumomin Babana da Wawa dake Ƙaramar Hukumar Borgu a Neja.

Jagoran ƴan ƙungiyar a wani saƙon murya ya yi barazanar kai hari ga ƙauyukan dake yankin, inda suka kashe mutane da kuma yin garkuwa da wasu da neman a biya su kuɗin fansa a yayin ayyukansu.

By Babaji