
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar haɗaka ta bada gurbin karatu ga ɗaliban da ke kammala sakandare (JAMB) ta ce za a fara rubuta jarrabawar UTME na shekarar 2025 a ranar 24 ga Afrilu a madadin ranar 25 ga watan da ta sanar da baya.
A wata sanarwa da Kakakinta Fabian Benjamin ya fitar a ranar Asabar, hukumar ta ce ta yi hakan ne don maslahar ɓangarorin da ta ke aiki tare da su.
Ya ce, akwai buƙatar ɗaliban su sake fitar da takardar jarrabawar a komfuta don sanin haƙiƙanin yadda sabon jawabin ya ke.
Takardar ta ƙunshi wuri, lokaci da wasu bayanai da ake buƙatar ɗalibi ya sani game da jarrabawar.
Ya kuma yi kira a gare su da su fara fitar da takardar daga yau Asabar ta adireshinta.
Ga tsarin da za a bi wajen fitar da takardar kamar yadda Blueprint ta ruwaito: “How to Print Your Notification Slip: 1. Visit www.jamb.gov.ng. 2. Click on “2025 UTME Slip Printing.” 3. Enter your registration number and click on “Print Examination Slip.”
