HOTUNA: Shettima ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Marigayi Galadiman Kano, Abbas Sanusi

Spread the love

Mataimakin Shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima, wanda ya samu rakiyar Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif, ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalai da ƴan uwan Marigayi Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi, a gidansa da ke unguwar Sagagi a birnin Kano.

Shettima ya samu kyakkyawar tarba daga ɗaya daga cikin manyan ‘ya’yan marigayin kuma Shugaban Jam’iyyar APC naJjihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, da sauran ƴan uwansa maza da mata.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya yi addu’ar Allah ya jaddada rahama gare shi da sauran al’ummar Musulmi bakiɗaya.

By ukarofi