
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar ƴan sanda a Jihar Borno, ta yi nasarar kama wasu mutane takwas bisa tuhumar su da hannu a kisan wani jariri da binne shi a wani asibitin kuɗi dake yankin Kwatam a hanyar Baga dake Maiduguri, babban birnin jihar.
Kakakin rundunar, Nahun Daso ya bayyana hakan ga manema labarai a Maiduguri, ranar Asabar.
Ya ce, lamarin ya auku ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 1 na rana, a lokacin da wasu shaidu suka kira ƴan sanda domin sanar da su batun.
Daga lokacin ne jami’ansu suka kai same asibitin tare da kamo waɗanda ake zargin a wajen da abin ya faru.
Ya kuma ce, an tono gawar jaririn domin yin bincike a kai.
Tuni aka garzaya da waɗanda ake tuhumar Cibiyar Manyan Laifuka ta jihar (SCID) don faɗaɗa bincike kan al’amarin.
Kazalika, ya yi da kira ga al’umma da su cigaba da bai wa ƴan sanda haɗin-kai wajen ruwaito sahihan bayanai game da al’amuran da ke faruwa a yankunansu don ɗorewar zaman lafiyarsu.
