Katsina: ‘Yan bindinga sun kashe limami da garkuwa da mamu 10

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wasu mutane ɗauke da muggan makamai da ake kyautata zaton ɓarayin daji ne sun kai hari a wani masallaci da ke unguwar Tudun Malamai a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina, inda suka kashe limamin da ke jagorantar Sallar Isha’i tare da yin garkuwa da aƙalla masallata goma.

Lamarin dai ya faru lokacin da mutanen ke gudanar da sallar isha’i, harin ya kuma yi sanadin jikkata wasu mutane biyu.

ɗan jarida mai sharhi kan sha’anin tsaro  Bakatsine ya wallafa a bayanai game da yadda ɓarayin suka yi dirar mikiya a masallacin.

“A daren jiya ne ( Laraba) wasu ‘yan bindiga suka kai hari a yayin Sallar Isha’i a unguwar Tudun Malamai da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina. 

“Sun kashe limamin da ke jagorantar sallar, sun raunata mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu masallata aƙalla 10 a yayin harin,” inji shi.

Har zuwa haɗa wannan rahoton, rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ba ta fitar da yi ƙarin haske ba dangane da faruwar lamarin.

By ukarofi