Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PRP na Arewa Maso Yamma, Injiniya Abba Sule Namatazu, ya bayyana cewa, masu neman yin haɗakar jam’iyya ko maja da jam’iyyar PRP ‘yan jari hujja ne kuma yawancinsu da suke ƙoƙarin haɗa majar sune kan gaba wajen karya Nijeriya da kuma dimukraɗiyya domin a cewarsa, yawancinsu sun fito ne daga jam’iyyu da su ka kasa inganta rayuwar al’ummar Nijeriya, “domin za ka ga daga mutanen PDP sai mutanen APC da sauransu wanda kowa yasan ‘yan jari hujja ne kuma su suka maida Nijeriya baya maimakon gaba idan aka yi la’akari da matsin rayuwa na rushewar tattalin arziki da rashin tsaro da rashin hasken wutar lantarki, rashin ingantacen ilimi, lafiya, noma, cin hanci da rashawa da sauransu.
“To kuma sune a yanzu suke so m uzo mu ba su rijistar jam’iyyarmu ko mu zo mu yi haɗaka da su da sunan maja, to wannan dalili ne ya sa mu da muke jam’iyyar PRP wadda ta samo asali daga jagoran talakawa Malam Aminu Kano aƙidarsa ce ceton talakawa ne daga rashin ‘yanci zuwa ‘yanci, daga talauci zuwa wadata, daga jahilci zuwa ilimi daga sukurkucewar al’amura zuwa inganta su a kowanne fanni. Wannan ita ce aƙidar Malam Aminu Kano kuma ita ce aƙidar jam’iyyar PRP da muke so al’ummar Nijeriya su bata shugabanci a 2027 in Allah ya kaimu su ga aiki da cikawa, amma dai a halin yanzu jam’iyyar PRP ba za ta yi maja ko haɗaka da ‘yan jari hujja ba.”
Injiniya Abba Sule Namatazu mataimakin shugaban jam’iyar PRP mai kula da Arewa a lokacin da yake ƙarin haske a lokacin bayan kammala taron shekara-shekara da cibiyar nazarin dimukraɗiyya ta Mumbayya da ke ƙarkashin Jami’a Bayero ta shiryawa wanda aka yi a karo na 23 wacce kuma ta zo daidai da cika shekaru 42 da komawar Marigayi Malam Aminu Kano ga mahalicinsa a 1983 wanda aka gabatar a ranar Alhamis ɗin da ta gabata a gidan Mumbayya da ke unguwar Gwammaja a birnin Kano.
Haka kuma ya ƙara da cewa akwai buƙatar talakawa su waye su guji siyasar karɓar kuɗi ko kayan abinci a lokacin zaɓe domin hakan baya haifar da ɗa mai ido a dimukraɗiyya, shi ne kuma ya zama tushen koma baya wanda yake bayan jari hujja damar baje hajarsu na cigaba da mulki mara maana maimakon a samu cigaba shekaru 25 da dawowar dimukraɗiyya kullum gwara jiya i yau wannan abin takaici ne inda kuma ya yabawa cibiyar nazarin dumukraɗiya kan shirya irin wannan taruruka don wayar da kan alumma wajen kawo ingantaciyar dumukraɗiya da za ta bunƙasa tsaro da tattalin arziki a ƙasar mu inda kuma yayi addua samun rahama ga Maragayi Gwarzon talakawa Malam Aminu Kano da ɗaukakin al’ummar Ma’aikin Allah.
Wannan taro na bana na tunawa da Malam Aminu Kano shekaru 42 da rasuwa ya samu halartar shugabanin, yansiyasa na da dana yanzu da masana daga jamioi da cibiyoyin ilimi wanda kuma aka tattauna matsaloli akan sabuwar dokar haraji wacce ta yamutsa hazo a Nijeriya.
A jawabinsa na babban mai jawabi a taron Farfesa Kabiru Isa Dandago masani akan ƙididiga a jamiar Bayero ya ce shawarwarin da suka bayar a kan wannan doka yanzu a samu raguwar kashi 80 cikin 100 na matsalolin ya ƙunsa mudin shugaban ƙasa ya sa hannu akan yadda aka tsara dokar daga cikin wanda suka tofa albarkacin bakin su akwai Farfesa Badawi M Sani daga BUK sai Sanata Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila sai kuma shugaban taron Farfesa Abubakar Adamu Rashid tsohon shugaban NUC daga cikin shugabani akwai gwamnan Kano Injinya Abba Kabir Yusuf wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Kwamarad Abdulsalam Aminu Gwarzo inda shugaban cibiyar Farfesa Abu Muhammad Fagge ya bayyana gamsuwar sa kan wannan taro da cibiyar da ke ƙarkashin jamiar Bayero ƙarkashin shugabancin Farfesa Adamu Abbas ta ke shiryawa duk shekara.
