Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi ya ayyana cewa, ba zai yiwu ba Gwamnatin Jihar Kebbi tana bai wa kamfanin samar da wutar lantarki na Kaduna (KAEDCO) zunzurutun kuɗi har Naira miliyan ɗari da hamsin kowane wata sannan kuma a ce al’umma ba za su mori kuɗinsu ba.
Gwamnatin Jihar Kebbi tana da wani kwamiti ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Gwamnan Jihar, Sanata Umar Abubakar Argungu (Tafidan Kabi), don gano musabbabbin rashin samun wadataccen wutar lantarki a jihar.
Ya ƙara da cewa, yanzu haka akwai unguwannin da ba sa wuce samun wutar na sa’o’i uku kacal ba a cikin sa’o’i ashirin da huɗu ba.
“Wannan fa yana daga cikin alƙawurran da mu ka yi wa al’umma lokacin yaƙin neman zaɓe saboda haka muna sane da matsalolin da ke addabar su kuma ba za mu rungume hannu muna kallo ana matsar da su ba ba gaira ba dalili, muna sane da wannan wutar akwai ta kuma ba wata matsala ce ta faru ba saboda haka ba wani dalilin hana su samun wutar lantarki.”
Wata takarda mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin samar da wutar lantarki na jihar Kebbi Abdulaziz Abdullahi ta bayyana cewa kamfanin ya yaba wa gwamnan bisa ga kulawarsa ga al’umma bayan wannan kuma ta ƙara da cewa yanzu haka hukumar tana bayar da wutar naira biliyan goma amma a cikin watanni bakwai amma billiyan uku kaɗai ta samu wanda duk da haka bai hana ta gudanar da ayyukanta ba.
Haka-zalika takardar ta ƙara da cewa yanzu haka kamfanin yana nan yana ‘yan gyare-gyare don ganin ta inganta samar da wutar lantarki ga jama’a.
Wutar lantarki dai yanzu ta zama tamkar wani zinare saboda ba ko’ina ake samun ta ba kuma idan an samu wutar bai wuce sa’a ɗaya ba zuwa biyu ba shi kenan kuma sai gobe wanda yanzu haka ya yi sanadiyyar rashin ruwan sha da a gidaje da a kullum tun da safe za ka ga mutane suna gararamba da kayan ɗibar ruwa.
