Assalam alaikum. Ina yi wa Edita barka da wannan rana, Allah ya ƙara basira da ɗaukaka, ya kuma albarkaci jaridar Blueprint Manhaja.
A wannan zamani namu na yau, yawan baƙin ciki da damuwa, wato depression and anɗiety, a Turance, sun yi yawa kwarai a cikin al’umma, musamman ma matasa. Dalilai da dama kan haifarwa mutane – yara ƙanana, da matasa, kai harma tsoffi na shiga halayya na damuwa da baƙin ciki. Hakan kan iya ta’azzara ya zame musu cututtuka da suka shafi kwakwalwa wanda ke iya yin mummunar tasiri a rayuwarsu.
Matasa kamar ’yan makaranta irin jami’o’i da sauran manyan makarantu sun fi kowa shiga irin wannan matsala. Domin kuwa basu yi hankalin da manya ke da shi ba na iya juriya da irin yanayi na rayuwa da kan sami mutum. Za ka ga cewa daga zarar wani ɗan matsala ta damuwa ko ɓacin rai ya same su sai su bi su kwallafa abin a ransu har ya zame musu irin wannan cutar na depression da anɗiety.
Wai shin ya ya yawaitar wannan cutar ta baƙin ciki (depression) ya ke ne?
A wani bincike da aka yi ba da jimawa ba a wani mujallar lafiya ta ƙasar Amurka mai suna ‘American Journal of Psychiatry’ a Turance, an bayyana wasu ƙididdiga masu ban mamakin gaske game da wannan matsala. A faɗin wannan binciken, yawan yara ’yan makarantan sakandare har izuwa matasa da ke gaba da sakandare masu fama da wannan cuta ta depression ya yi tashin gwauron zaɓi. ƙididdigar ya ce, alƙaluman sun tashi daga kashi 3.3% cikin ɗari har izuwa 7.06% cikin ɗari daga shekarar 1991 zuwa shekarar 2020 — shekara ashirin ke nan idan shekarar 2020 ta tsaya. ƙarin da aka samu ya kusan tasarma kashi 50% ke nan cikin ɗari duk a cikin shekaru ashirin.
Me ke janwo ciwon baƙin ciki ne?
1. Shiga wani tashin hankali da kan taɓa kwakwalwa ko ma jiki (mental or physical trauma).
2. Samun koma baya ko kuma rashin nasara a rayuwa.
3. Sakin aure ko kuma rashin wani masoyi, misali, rashin ɗan uwa haka.
4. Yawan shiga matsala da tashin kanlali (stress and tension).
5. Mutumin da ya fuskanci cin zarafi da ya shafi fyaɗe ko makamancin hakan (wannan kan shafi mace ko namiji).
6. Kyankyani da ke farawa daga yaranta da kuma tsoro na ba gaira babu dalili (phobias and irrational fear).
7. Cin zarafi da wasu kan fuskanta a cikin gida, wato domestic ɓiolence, a Turance.
Ya ya ake gane mutum na fama da ciwon baƙin ciki?
Gano mutum mai fama da ciwon baƙin ciki abu ne mai wuya, saboda yawanci mutane basu son bayyana damuwarsu ga idon duniya. Sai ka ga mutum na farin ciki da nuna jin daɗi a filli, amma a ciki labarin daban ya ke. Amma tabbas in har wannan cutar ta tsananta, alamu zai fara nuni a jikin mai ɗauke da ita. Ga wasu daga cikin alamun cutar:
1. Rama mai tsanani ko kuma ƙarin ƙiba cikin lokaci ƙanƙani.
2. Mutum ya riƙa jin rashin daɗin zuciyarsa, ko baya iya ɗaukan mataki (indecisiɓeness), ko kuma jin takaici da makamantan waɗannan yanayi.
3. Rashin ganin darajar kai (low self-esteem) da kuma rashin iya taɓuka abin kirki.
4. Rashin bacci ko kuma yawan baccin.
5. Rashin jin daɗin abinci, ko fama da kasala da yawan rashin lafiya.
Za mu cigaba a mako mai zuwa, Insha Allah.
Wassalm.
Wasiƙa daga MUSTAPHA MUSA MUHAMMAD, 09123302968.
