Bacci a jikin ɗan adam

Spread the love

Tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

’Yan uwa masu karatu, assalamu alaikum. Barkan mu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi da ke kawo mu ku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. Idan kun shirya, bismillah.

Maƙalar yau, in sha Allah, za ta yi duba ne izuwa wani abu mai matuƙar muhimmanci a jikin ɗan Adam, amma saboda yanayin yadda al’ummarmu ta ke, da kuma a ɗabi’ance mun yarda bacci zai zo ko ba mu nemeshi ba, mutane da dama ba su san komai ba dangane da rawar da bacci yake takawa a jikin ɗan Adam ba. A lissafina ban da da masana lafiya da likitoci, saboda su dole ne su san wani abu dangane da bacci a rayuwar mutum.

Bacci rahama ne daga Rabbul Izzati, ba za mu fuskanci hakan ba sai lokacinda muka kasa bacci. Kamar yadda na sha faɗa a mafi yawan rubutuna, ita ƙwaƙwalwar mutum Allah ya yi ta ne, domin ta karɓi saƙonnni daga abubuwan da ke kewaye da mu, sannan daga bisani ta yanke hukunci. An mata tsari na taskance bayanai da yin amfani da bayanan domin fassara abinda zai iya wakana a yanayi na gaba. Saboda wannan dalili, babu wani ɗan Adam da zai tsaya yana tunanin hanyoyin da zai bi domin yayi bacci, matuƙar lafiyayye ne. Lokacin baccin yana shiga bacci zai kwashe mutum.

Kowa yana bacci, sai dai kuma kowa da irin yadda yanayin baccinsa ko baccinta ya ke. Baccin yara ya shan banban da na matasa; kamar yadda baccin matasa ya banbanta da baccin dattijai da tsofaffi. Zan kawo bayani insha Allah idan ana biye da ni.

A matsayina na dalibi mai neman sani, ba zan iya zayyana komai da komai da ya danganci bacci ba; amma zan yi iya ƙoƙarina wajen fahimtar da ku ɗan abinda na sani. Haƙiƙa bacci maudu’i ne mai faɗin gaske, wanda ya ke da alaƙa da rayuwar ɗan adam ta fuskoki da dama irinsu: nutusuwa, hankali, ganewa, azanci, fahimta, saiti, da sauransu. Haka kuma yana da alaƙa da lafiyar gaɓɓan jiki irinsu zuciya, ƙwaƙwalwa, kayan ciki, jini, da sauran gaɓɓai.

Saboda muhimmancin bacci a rayuwar ɗan adam, a ƙasashen da su ka cigaba, nazari da bincike a ke yi na musamman akansa. Akwai wata gidauniya mai suna “Sleep Foundation” a birnin Washington da ke ƙasar Amurka. Aikin wannan gidauniya shi ne ilmintarwa da wayar da kan jama’a, da bayar da shawarwari game da bacci, da illolin da suke tattare da rashinsa ko ƙarancinsa,  da bincike akan yadda za a inganta shi. Wannan lamari ya ƙara ba ni ƙwarin gwuiwar yin rubutu akan bacci.

Wani farfesa masanin kimiyyar ƙwaƙwalwa da tunanin ɗan Adam mai suna Matthew Walker, ɗan ƙasar Amurka, ya wallafa littafi mai suna “Why We Sleep”, ma’ana: ” Me Yasa Mu Ke Bacci”. Littafin ya bayyana a shekarar 2017 inda ya ɗauki hankalin duniyar masu karatu. A cikin littafin, ya kawo bayanai da dama na yadda bacci ya ke ɗamfare da rayuwarmu, ya kuma kawo hujjoji na kimiyya da suke kewaye da bacci. Bai tsaya a nan ba, ya kawo bayanin tasirin bacci a jikin ɗan adam, da abinda rashin baccin kan iya jawowa. Har ma ta shiga bayani game da yadda mafarki ya ke wakana. Ku dai biyo ni sannu a hankali domin ƙarin bayani.

To, da fatan dai har yanzu kuna biye da ni. Yanzu bari mu fara da tambayar kanmu: Shin me ne ne bacci? Bacci wani yanayi ne wanda jiki da ruhin ɗan Adam su ke shiga domin hutawar jikin da ruhin daga gajiyar da ta yi ɗawainiya da shi tsawon wannan wuni. Bacci yana faruwa ne kowacce rana, inda a ɗabi’ance, yafi fi faruwa yayin da wuni ya ƙare, dare ya shiga.

Tambaya ta biyu: Shin Yaya yanayin bacci ya ke? Idan ɗan adam zai shiga yanayin bacci,  zai rufe idanunsa ko idanunta, gaɓɓan jikinsa za su shika, tsokar nama ta sassan jikinsa za su sakata (musamman masu motsawa yayin gabatar da manyan al’amura irinsu tafiya, gudu, magana, da sauransu), wartsakewarsa za ta gushe. Shi ya sa idan ɗan adam ya na bacci, to fa a tsakiya yake: tsakanin rayuwa da mutuwa; tsakanin mai hankali da marar hankali; tsakanin zahiri da gaibu.

Tambaya ta gaba: Shin akwai nau’i na bacci? Amsa : E, akwai. Da Hausa mu na kiransu da (a) Bacci sassauƙa da (b) Bacci nannauya. A addinance kuwa kala huɗu ne : Dogo mai nauyi; Dogo mai sauƙi; Gajere mai nauyi; da kuma Gajere mai sauƙi. A turance ana kiransu: Rapid Eye Moɓement Sleep (REMs), da kuma Non-rapid Eye Moɓement Sleep (NREMs).

Yayin da mutum ke bacci sassauƙa marar nauyi, a wannan yanayi wartsakewarsa ba ta gama barin jikinsa ba. Shi ya sa za ka ji mutum ya ce: “ai kafin bacci ya ɗauke ni ɗazu, ina jinki kuna maganar kaza-da-kaza”. A wannan lokaci, baccin bai gama kama shi ba ne. Amma a lokacin da bacci mai nauyi ya kama mutum, babu wani abu da zai iya ji ko ya gani, ko ya fahimta.  Dalili kuwa shi ne  ba a farke ya ke ba;  gaba daya wartsakewarsa ta tafi. Saboda bambanci tsakanin yadda Sarkin halitta ya halicci mutane, akwai waɗanda saboda tsabar nauyin baccinsu, za ka iya ɗaukarsu kacokan ka sauya musu wajen kwanciya ba tare da sun farka ba. Ka ji ikon Allah!

Shin ko bacci ya na da matakai? A wani bincike na masana, sun yarda cewa bacci yana da matakai guda huɗu: Mataki na farko shi ne lokacin da mutum yake tsakanin a cikin bacci da kuma a farke. A wannan mataki ne tsokar jikinka za ta shika, saurin wulgawar idanunka zai ragu, saurin bugun zuciyarka ya ragu, kuma saurin fitar numfashinka ya ragu shi ma. Yanayin yadda ƙwaƙwalwa ke sarrafa ayyukanta da bada umarni shi ma zai ragu. Yayin da ɗan Adam ya kwanta bacci, ya kan ɗauki mintuna a cikin wannan mataki.

A mataki na biyu kuwa, baccin zai fara nauyi; jikinka zai ƙara shikawa; idanunka za su rage motsi sosai ko su daina; numfashinka zai dinga fita a hankali, ita ma zuciyarka za ta dinga bugawa a hankali. Haka kuma zafin jikinka (body temperature) shi ma zai ragu sosai. Wannan mataki na bacci ya fi duka sauran tsayi in ji masana.

Mataki na uku kuwa, a cikinsa ne bugun zuciya da fitar numfashi za su ƙure iyakar hutawarsu. Wannan mataki na da alaƙa da wajen sanya wa ɗan Adam kuzari da wartsakewa bayan ya farka daga bacci.

Mataki na ƙarshe shi ne wanda a cikinsa idanu za su dinga mommotsawa da sauri (REMs) Gudun jini a magudanansa zai fara ƙaruwa; zuciya za ta ɗan fara bugawa da sauri fiye da daa, shima numfashi zai ɗan ƙara sauri. Wannan mataki ya kan fara ne yayin da mutum ya samu kimanin awa ɗaya da rabi yana bacci.  An yi ittafaƙin cewa a wannan mataki ne mafarki yake faruwa yayin da ɗan adam ya ke bacci. A wannan mataki na bacci, Allah cikin ikonsa sai hannaye da ƙafafuwa su sage. Hikimar hakan shi ne kar mutum ya dinga ayyana abinda yake yi a mafarki da Gaɓɓansa a zahiri.

By ukarofi