Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Matsalar ƙarancin hasken wutar lantarki a Jihar Kano, wanda yanzu ta shiga makonni, ta kawo cikas ga harkokin zamantakewar al’umma a cikin babban birnin jihar, lamarin da ya jefa al’umma da masu kasuwanci cikin tsananin ƙunci.
Mazauna Kano, jihar da ta fi kowacce yawan al’umma a Nijeriya da jihohin Jigawa da Katsina suna ci gaba da ɗawainiya kan rashin wutar lantarki.
Hakan ya biyo bayan yawan ɗauke wutar da kamfanin rarraba wutar lantarki da ke Jihar Kano (KEDCO) ke yi. Wasu mazauna Kano sun ce, wutar da suke samu ba ta wuce sa’o’i biyu zuwa uku a kullum ba, a kwanaki da yawa da suka gabata.
Mazauna jihohin uku na daga cikin jihohin da ke fuskantar yanayi na zafi a arewacin ƙasar, lamarin da ya sa ake matuƙar buƙatar wutar don sanyaya abubuwan sha da abinci da gidaje ko shagunansu.
Hakan na zuwa ne yayin da ƙananan masana’antu ke fuskantar matsaloli sakamakon ƙarancin wutar lantarkin.
Lamarin da ya kai ga durƙushewar wasunsu tun a baya.
Rashin lantarkin, wanda ke da nasaba da katsewar babban hasumiyar lantarki, ya jefa al’umma cikin duhu, abin da ya tilasta wa ‘yan kasuwa dogaro da wasu hanyoyi masu tsada wajen samun lantarki da kuma jefa mutane da yawa cikin matsalar kuɗi.
Da suke zantawa da manema labarai, mazauna yankin da dama sun koka da tasirin katsewar lantarki.
Wani mai babban kanti kuma mai gidan abinci a Sabon Gari, ƙaramar hukumar Fagge, Jude Michael, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici. “Na yi kwanaki ina amfani da janareta, wanda hakan ke janyo min asara.
“Wani lokaci abokan ciniki suna zuwa, wasu lokuta kuma ba sa zuwa. Ba kowane lokaci ake samu kwastoma ba. Abin babu daɗi,” inji shi.
Wani mai walda a garin Dakata a ƙaramar hukumar Nasarawa, Abubakar Bala, ya ce kasuwancin sa ya gurgunta. “Mun biya kuɗin wutar lantarki, amma ba mu samu ba, idan ba a dawo da wutar lantarki nan da nan ba, kasuwancina na iya rugujewa,” inji shi, yana mai kira ga gwamnati da ta gyara matsalar tare da yin la’akari da wasu hanyoyin samar da makamashi.
A ƙaramar hukumar Tarauni, wani mai walda, Aminu Sani, ya ce tsadar man fetur ya sa ya dakatar da aiki. “Muna cajin kuɗi da yawa lokacin amfani da janareta, amma ba kowa ba ne zai iya samun biya. Yanzu mun maƙale,” inji shi.
Dillalin sayar da abinci masu ƙanƙara, Manu Garba, wanda ke ɗaura da hanyar Zariya, ya ce ’yan kasuwa tsunduma cikin bashi. “Mun ci burin samun ciniki a lokacin bikin Easter, amma kaji da kifi sun lalace,” inji shi.
A garin Kumbotso, wata mai salon gashi, Fatima Usman, ta koka da yadda kamfanin samar da wutar lantarki ke ci gaba da bayar da takardar biyan kuɗi duk da katsewar. “Wannan babban rauni ne ga waɗanda suka dogara da wutar lantarki don samun kuɗi,” inji ta.
A halin da ake ciki, masu yin cajin wayar hannu sun ba da rahoton ƙarin kuɗi. Malam Isa Umar ya ce ya ƙara farashin tsakanin N150 zuwa N200 a kowace waya saboda kuɗin mai.
