Daga UMAR AKILU MAJERI Dutse
Hukumar hana sha da fatauchin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa reshen Jihar Jigawa ta sami nasarar kama wasu Motoci maƙare da miyagun ƙwayoyi waɗanda ake zargin ana yin safararsu ana kai wa jihohin Jigawa, Yobe, Bauchi da Jamhuriyar Nijar.
Shugaban hukumar a Jihar Jigawa Alh Musa Marina shine ya sanar da taron manema labarai haka a ofishinsa dake birnin Dutse fadar gwamnatin jihar ta Jigawa.
Alh Musa yace hukumarsa ta sami bayanai masu ƙwari akan yadda dilolin miyagun ƙwayoyi suke bin hanyar Gumel zuwa Birniwa kuma suke kasafta miyagun ƙwayoyi a kwanar dole aana sayarwa masu safararsu zuwa jihohin Yobe ,Bauchi da Jigawa da kuma Jamhuriyar Nijar.
Shugaban hukumar yace bayan sun sami dukkan bayanai na sirri akan yadda masu fasa ƙaurin miyagun ƙwayoyi suke cin kasuwarsu a Jihar Jigawa shine suka kafa shingaye a kan hanyar mota zuwa Gumel inda da misalin karfe tara na dare a ranar 25/4/2025 suka kama wata mora kirar siyana maƙare da miyagun ƙwayoyin tramadol da ƙwayoyi preegabalin.
Waɗanda dukkansu ƙwayoyine masu haɗarin gaske ga rayuwar al’umma sakamakon haka hukumar ta kama wani mutun da ake zargin direban motarne da kuma wani mutun guda da yakewa ƙwayoyi rakiya zuwa kwanar dole dake cikin ƙaramar hukumar Birniwa inda anan ne ake kasafin ƙwayoyi kowacce nahiya ta ɗauki kasonta.
Kama wannan tarin kwayoyi yasa jami an hukumar suka tsaurara bincike akan daga inane tushen ƙwayar ya ɗauki asali , sakamakon haka yasa aka garzaya wani gida dake unguwar Mil Tara a ƙaramar hukumar Ungogo dake cikin birnin Kano inda aka kama wani magidanci a gidansa yana tare da iyalinsa da wata mota kirar homa bus itama maƙare da ƙwayoyi na preegabalin da tramadol wadda ita ake zargin zatabi bayan waccan siyana zuwa Jihar Jigawa domin cimma manufarsu.
Anyi kiyasin yawan kuɗin ƙwayoyi zai naira biliyan biyu da miliyan ɗari shida wato N2.6 billion kuma nauyin ƙwayoyi yakai 1781 million kg.
Maina ya ƙara da cewar da zarar sun kammala bincike zasu gurfanar da waɗanda suka kama ɗin a gaban kotu domin su girbi abinda suka shuka domin hakan ya zama izina ga masu sha awar aikata irin wannan ɗanyen aiki.
