Daga USMAN KAROFI
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ayyana Alhamis, 1 ga Mayu, 2025, a matsayin hutu don bikin ranar ma’aikata a Najeriya.
Tunji-Ojo ya jinjina wa ƙwazon ma’aikata da sadaukarwarsu, yana mai cewa ƙoƙarin su ne ke ba da gudunmawa wajen gina ƙasa da kuma samun girma a idon duniya.
Ya kuma jaddada buƙatar zaman lafiya a tsakanin ma’aikata da gwamnati don tabbatar da ci gaba da haɓakar tattalin arzikin ƙasa.
