
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa, NiMeT, ta yi hasashen samun hasken rana da hadari mai ɗauke da tsawa daga ranar Laraba zuwa Juma’a a sassan Nijeriya.
A hasashen nata na ranar Talata, NiMeT ta yi nuni da cewa, za a samu hasken rana a ranar Laraba a yankin Arewa.
Haka kuma, za a samu hadari da tsawa a lokutan rana da yamma a yankunan Jihohin Kaduna, Adamawa, Sakkwato, Kebbi, Zamfara da Taraba.
A Jihohin Abuja, Benue, Kwara, Neja, Filato da Kogi kuwa, za a samu hadari da yiwuwar tsawa a lokacin rana da kuma yammaci.
A kudancin ƙasa kuwa, za a samu hadari mara ƙarfi a Jihohin Delta, Kuros-Riba, Akwa-Ibom, Ribas da kuma Bayelsa a lokacin safiya.
NiMeT ta kuma yi kira ga al’umma da su kiyaye musamman a wuraren da ake sa ran samun ruwan sama mai ɗauke da iska da tsawa yayin da suke shirya gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
