FBI da wasu hukumomi za su saki rahoton zargin ta’ammali da ƙwayoyi akan Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Juma’a, 2 ga watan Mayu, 2025 ne ake sa ran hukumomin gwamnatin Amurka da suka haɗa da Cibiyar Bincike ta FBI da DS da wasu za su fitar da rahoton zargin ta’ammali da ƙwayoyi akan Shugaba Bola Tinubu tun a shekarun 1990s.

A farkon watan Afrilu ne kotun Amurka ta ‘District’ a madadin takwararta ta ƙasar Colombia ta umarci sauran hukumomin da ke da hannu a batun, ban da CIA, da su shirya baki ɗaya bayanan da ke da alaƙa da batun tare da fitar da rahotonsu a ranar 2 ga watan Mayu.

Hakan ya biyo bayan nuna buƙatar bada bayanai kan batun ne la’akari da ƴancin sanar da al’umma da tabbatar da adalci, kamar yadda Greenspan, wanda ya shigar da ƙarar neman fitar da bayanan a shekarar 2023 ya bayyana.

Ya ce, lallai Amurkawa da ƴan Nijeriya suna da ƴancin sanin cikakken tarihin wanda ke shugabantar su.

Greenspan ya kuma zargi hukumomin da gaza fitar da takardun bayanan a lokacin da aka ƙayyade masu, wanda hakan ya saɓa wa dokar FOIA.

Musamman ya nemi a fitar da bayanan zargin Shugaba Tinubu da wasu mutane uku da suka haɗa da Lee Andrews Edwards, Mueez Adeboyega Akande da Abiodun Agbele a laifin ta’ammali da safarar ƙwayoyi tun tsawon kimanin shekaru 30 da suka gabata.

By Babaji