Yar asalin Jihar Katsina ta zama daraktar kasuwanci a kamfanin NNPC

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Kamfanin mai na ƙasa (NNPC), ƙarƙashin jagorancin Bayo Ojulari, ya naɗa hajiya Maryam Idris Bagiwa wata ‘yar asalin Jihar Katsina a matsayin daraktar kasuwanci na kamfanin.

Hajiya Maryam Idris Bagiwa za ta jagoranci harkokin kasuwancin sayar da ɗanyen man fetur na Najeriya, tare da kula da dabarun ciniki a cikin gida da ma ƙasashen waje.

Masana tatttalin arziki sun bayyana cewa wannan muƙami da aka bai wa Bagiwa, yana da matuƙar muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin ƙasa, kuma yana nuna yadda Jihar Katsina ke ci gaba da samar da shugabanni nagari a matakin ƙasa.

Tuni jama’a a ciki da wajen Jihar Katsina da kuma kafafen sadarwa na zamani, suka fara taya ta murna bisa wannan sabon matsayi da Allah ya bata.

By ukarofi