Daga JAMIL GULMA a Kebbi
ƙarshen makon da ya gabata wata budurwa mai kimanin shekaru 16 ta rasu sanadiyyar kifewar kwale-kwale a Argungu da ke Jihar Kebbi.
Hatsarin dai ya afku ne da yammacin ranar Lahadin da ta gabata a Mashayar Gobirawa lokacin da manoma ke dawowa daga gona.
Wani da abin ya faru a gaban idonsa ya bayyana cewa dama duk lokacin da mutane ke dawowa daga gona da yamma a kan samu cinkoso wajen shiga kwale-kwale saboda haka wani lokacin mutane su kan yi wa kwale-kwalen yawa har sai ya rinƙa ɗibar ruwa daga gefen sa, wannan ma haka ne ya yi sanadiyyar rasuwar wannan yarinya saboda jirgin kwale-kwalen an yi masa yawa bayan an soma tafiya sai ya rinƙa ɗibar ruwa daga gefe daga nan sai kowa ya yi ta kan sa ita kuwa wannan yarinya ta nutse.
“Lokacin da aka kawo agaji ta riga ta sha ruwa ta galabaita tare da sauran yara huɗu, saboda haka bayan an fitar da su ita ta rasu,” inji shi.
Malam Yusuf Mashaya shi ne mai kulawa da wannan mashayar ta Gobirawa ya kuma shaida wa wakilinmu da cewa gaskiya ne lamarin ya faru kuma wannan yarinya ɗaya Allah ya yi mata rasuwa.
Ya ƙara da cewa duk hidimar da suke yi wa al’umma rani da damina ba su taɓa samun tallafi daga wata hukumar ko wani ɗan siyasa ba duk da ya ke sun sha kai ƙorafi a ƙaramar hukumar mulki ta Argungu amma a banza.
Yanzu haka babu kwale-kwale ko ɗaya mai kyau a mashayar duk sun lalace dabaru kawai su ke yi.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Argungu Honarabul Aliyu Sani Gulma inda ya ce tun kafin wannan lokacin sun kai ƙorafi ga maigirma gwamna Nasir Idris kuma ya bayar da damar a siyo kwale-kwale hamsin da uku don a raba wa masu kulawa da ire-iren waɗannan wuraren tun daminar bara.
