Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Kwamanda Idris Jibrin ya fara aiki a hukumance a matsayin kwamandan hukumar tsaro ta NSCDC na 14 a Jihar Gombe, bayan ya gaji Kwamanda Gyama Gyawiya (mai ritaya), wanda ya yi ritaya bayan kai shekarun da doka ta tanada, wato shekara 60.
Bikin miƙa ragamar shugabanci ya gudana a ranar Juma’a, 2 ga Mayu, 2025, a hedikwatar hukumar NSCDC ta Jihar Gombe, inda aka tabbatar da sauyin shugabanci cikin kwanciyar hankali.
A cikin wata sanarwa da shugaban hulɗa da jama’a na hukumar NSCDC a Jihar Gombe, SC Buhari Saad, ya fitar, tsohon kwamandan, Gyama Gyawiya, ya bayyana jin daɗinsa bisa nasarorin da ya samu a lokacin shugabancinsa.
Ya yabawa haɗin kan jami’an hukumar tare da nuna godiyarsa da damar da shugaban kwamandojin NSCDC, Dokta Ahmed Abubakar Audi, ya ba shi.
“Girman kai ne a gare ni na yi wa ƙasa hidima, kuma ina alfahari da nasarorin da muka cimma. Ina mika godiyata ga shugaban NSCDC bisa damar da ya ba ni jagoranci,” in ji Gyawiya.
A jawabinsa tun farko, Kwamandan Idris Jibrin ya nuna godiya bisa damar da aka ba shi don jagorantar hukumar NSCDC ta Jihar Gombe, tare da yin alƙawarin ci gaba da aiki tuƙuru don ciyar da hukumar gaba.
“Ina da nufin ci gaba da inganta nasarorin da magabacina ya samu ta hanyar ƙarfafa ƙwarewa, ɗa’a, da haɗin kai a tsakanin jami’ai.
Aiki na shi ne kare muhimman kadarorin gwamnati da na masu zaman kansu tare da tabbatar da tsaro a Jihar Gombe,” in ji Jibrin.
Ya kuma nanata muhimmancin haɗin kai da masu ruwa da tsaki tare da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran hukumomin tsaro domin ƙara tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar.
Bikin ya haɗa da sanya hannu kan takardun miƙa ragamar shugabanci da miƙa tutar hukumar NSCDC, alamar sauyin shugabanci cikin nasara da lumana.
Tare da sabon hangen nesa ƙarƙashin jagorancin Kwamanda Idris Jibrin, hukumar NSCDC ta Jihar Gombe za ta ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyi tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
