
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Harkokin Jiragen ruwa, Adeboyega Oyetola ya gargaɗi masu amfani da kwale-kwale akan yin tafiya ba tare da sanya rigar ninƙaya ba a sassan Nijeriya.
Mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dakta Bolaji Akinola ya faɗi hakan a wata takarda, biyo bayan raba rigunan ninƙaya guda 3,500 da Ministan ya yi a Jihar Bayelsa, ranar Juma’a.
Ya ce, Gwamnatin Tarayya ta ware riguna guda 42,000 da ta umarci a raba a dukkanin jihohin Nijeriya domin rage raɗaɗi haɗurran kwale-kwale da ake samu akai-akai a wasu sassan ƙasar.
Ya kuma ce, yin tafiye-tafiye acikin ƴan Nijeriya abu ne mai muhimmanci ga al’amuransu na yau da kullum musamman waɗanda suke yi acikin ruwa, don haka ne gwamnati ta ga dacewar samar da hanyoyin ƙara ba su kulawa.
Ministan ya ƙara da cewa, Gwamnati ta koka kan yadda ake yawan samun haɗarin kwale-kwale wanda a saboda haka ne aka rasa rayuka da dukiyoyi da dama, lamarin da ya sa ta samar da shirin raba rigunan.
