Gwamnatin Bauchi ta sallami jami’an sanya wa makarantu ido bisa sakaci a aiki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Jihar Bauchi ta yanke korar baki ɗaya jami’an da ke kula da harkokin gudanar da makarantu (SSOs) a Ƙaramar Hukumar Bauchi bisa sakaci wajen tsare ayyukansu.

Shugaban Hukumar Ilimin Bai-ɗaya na jihar (SUBEB), Alhaji Adamu Muhammad Duguri ya bayyana hakan jim-kaɗan bayan gudanar da zagayen ba-zata a makarantun gwamnati dake babban birnin.

Ya ce, hukuncin ya zama wajibi ne a lokacin da suka gano cewa jami’an da lamarin ya shafa ba sa gudanar da ayyukansu yadda ya dace.

Ya bayyana cewa, aikin da aka ba su shine su sanya ido game da harkokin makarantun kuma su riƙa ruwaito rahoto lokaci bayan lokaci ga hukumar ilimi na yankin don ɗaukar matakin da ya dace.

Haka kuma, ya ce rashin tsare aiki ga jami’an ya haifar da fashin zuwa makaranta ga malamai da dama, wanda tsaiko ne ga koyar da ɗalibai.

Don haka ne Shugaban na SUBEB ya umarci Sakataren Ilimin makarantun Ƙaramar Hukumar da ya mayar da jami’an da lamarin ya shafa aikin koyar da ɗalibai a aji.

Ya kuma ce, duk jami’in da ya ƙi amincewa da hukuncin, an ba shi zaɓin ya ajiye aikinsa, ya na mai cewa gwamnati ba za ta lamunci haddasa koma-baya ba a ƙoƙarinta na samar da gyara a harkar ilimi a jihar.

By Babaji