Da Ɗumi-Ɗumi: Tsagin Jam’iyyar LP ya dakatar da Gwamnan Abia da Sanata Ireti da wasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Laraba ne Jam’iyyar adawa, LP, ta sanar da dakatar da Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, Sanata Ireti Kingibe, Sanata Darlington Nwokocha, Victor Afam Ogene, Amobi Ogah da Seyi Sowunmi.

An dakatar da su ne bayan karɓar sakamakon rahoton kwamitin bincike da aka kafa don aiki akansu bisa zargin su da yin zagon-ƙasa ga jam’iyyar.

A ranar 2 ga watan Mayu, 2025 ne majalisar zartarwar jam’iyyar ta kafa kwamitin mutane biyar ƙarƙashin jagorancin Mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dakta Ayo Olorunfemi da sakatarenta, Alhaji Umar Farouk Rano Ibrahim don su gudanar da bincike akan wasu mambobi da ake zargi da ayyukan da suka shafi zagon-ƙasa.

Baya ga miƙa rahoton binciken ne a ranar 7 ga Mayu, majalisar zartarwar ta yanke hukunci dakatarwar.

A sanarwar da Sakataren jami’yyar, Umar Farouk Ibrahim ya fitar, ya ce an dakatar da gwamnan da sauran mutanen da aka lissafo daga shiga dukkan harkokin jami’iyyar.

By Babaji