Siyasar Abuja: Shin babu maƙarƙashiyar siyasa a sake tada ballin zargin takardun bogin Maikalangu?

Spread the love

Daga PAUL OKAH

A daidai lokacin da zaɓen ƙananan hukumomi na 2026 ke ƙaratowa, ana sake tayar da wani tsohon zargi da aka riga aka kammala – cewa shugaban ƙaramar Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja (AMAC), Hon. Christopher Zakka Maikalangu, ya miƙa takardar kammala makarantar firamare na bogi.

Zargin, wanda ke fitowa daga wani mamba na jam’iyyar APC, Awalu Tanko Mohammed, ya zo ne duk da cewa kotu ta riga ta yi watsi da lamarin a shekarar 2022, kuma ofishin Ministan Shari’a na Tarayya (AGF) ya bayar da umarnin a dakatar da shari’ar gabaɗaya.

Tun bayan nasarar Maikalangu a matsayin shugaban AMAC a 2022 ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ɗan takarar APC a wancan lokaci, Hon. Murtala Usman Karshi, ya ƙalubalanci nasarar bisa zargin amfani da jabun takarda, amma kotun sauraron ƙarar zaɓe ta kori ƙarar bayan rahoton binciken ’yan sanda da ya ce babu gaskiya a ciki.

Amma a ranar 24 ga Maris, 2025, Auwalu Tanko ya sake shigar da ƙara a kotun majistare da ke Dutsen Alhaji. Wannan karo, a matsayin ƙara kai-tsaye ta laifi (Direct Criminal Complaint), yana neman kotu ta sake duba takardar Hon. Maikalangu.

Sai dai wata wasiƙa daga Ministan Shari’a, Chief Lateef Fagbemi, SAN, ta nuna cewa, wannan ƙara ba ta da ma’ana, domin an riga an yanke hukunci a kan ta kuma an miƙa batun ga Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, domin kammala komai. Rundunar ‘yan sanda ta FCT ma ta tabbatar da hakan cikin wata wasika da aka aike wa kotu.

Lauyoyin Maikalangu sun yi nuni da cewa, cigaba da sauraron wannan ƙara wani nau’i ne na cin mutunci ga tsarin shari’a da kotuna, domin ana maimaita abun da aka riga aka warware.

Ko wannan zargin na da alaƙa da siyasa?

Wasu na ganin sauyin sheƙar Maikalangu daga PDP zuwa APC a watan Afrilu 2025 ne ya janyo wannan sabuwar matsala. A cewar wani lauya a Abuja, Barrister Yakubu Musa, “Wasu ‘yan siyasa da ke tsoron karɓuwar Maikalangu a sabuwar jam’iyya suna ƙoƙarin rusa shi kafin lokacin zaɓe.”

Ya ƙara da cewa, “Yadda jama’a ke nuna goyon baya ga Maikalangu a AMAC na tayar wa da wasu hankali, shi ya sa ake ƙoƙarin ɓata masa suna da ƙararrakin da ba su da tushe.”

Kotun ta dage sauraron ƙarar zuwa ranar 23 ga Mayu 2025, bayan Maikalangu bai halarta ba sakamakon ganawar da ya je yi da likita a asibiti.

Daga ƙarshe kamar yadda masu lura da al’amura suka bayyana, wannan batu zai iya zama wani yunƙuri na siyasa domin rage ƙarfinsa a zaben 2026. Amma, har yanzu, dokoki da shaidu na nuna cewa, Maikalangu ya tsira daga wannan zargi tun tuni.

Aisha ASAS ta fassara

By ukarofi