Shugaban ƙungiyar ɗalibai ya nemi afuwar Seyi Tinubu 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban tsagin ƙungiyar ɗaliban Nijeriya (NANS), Atiku Abubakar Isah, ya janye iƙirarin da ya yi a baya kan Seyi Tinubu, ɗan Shugaba Bola Tinubu, inda ya amsa cewa zargin da ya yi ba gaskiya ba ne.

Atiku ya zargi Seyi Tinubu da Ministan Matasa da Ci gaban Wasanni, Ayodele Olawande, a cikin wani faifan bidiyo da ya bazu, da cewa sun gayyace shi zuwa Legas kuma sun ba shi tayin Naira miliyan 100 domin ya mara wa Shugaba Tinubu baya, wanda ya ce ya ƙi karɓa, lamarin da ya haifar da sace shi a ranar 15 ga Afrilu, 2025.

Sai dai a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, Atiku ya nemi afuwa daga Seyi Tinubu, yana mai cewa labarin da ya bazu ƙarya ne. Ya danganta zargin da ya yi ga wani Ladoja Olusola wanda ya ce ya ba shi bayanan ƙarya don cimma manufarsa ta karƙe mulki a cikin ƙungiyar ɗaliban.

Ya rubuta cewa, “Yanzu ya zama dole a fayyace cewa batun tayin Naira miliyan 100 da aka ce an yi mini domin in mara wa Shugaba Tinubu baya, ƙarya ce tsantsa, kuma Ladoja Olusola ne ya shirya wannan ƙarya domin cimma burinsa na karɓe shugabancin ƙungiyar daliban Nijeriya (NANS) ta hanyar yaudara.

“Haka kuma, Ladoja Olusola ne ya ce mini cewa Seyi Tinubu zai iya umartar a kashe ni, sannan ya umurci Sufeto Janar na ‘yan sanda, Mista Kayode Egbetokun, da ya rufe batun.”

Atiku ya kuma janye zargin da ya yi a baya cewa Seyi Tinubu ya jagoranci ‘yan daba zuwa wurin bikin rantsar da shi, yana mai cewa Seyi bai taɓa halartar wurin ba.

By ukarofi