Tsarin jam’iyya ɗaya a Nijeriya ba zai haifar da ɗa mai ido ba, inji Jonathan 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban ƙasar Nijeriya, Goodluck Jonathan ya ce ƙoƙarin komawa tsarin jam’iyya ɗaya ta hanyar “ƙarfa-ƙarfar ar siyasa” zai jefa ƙasar cikin rikici.

Manhaja ta rawaito cewa Jonathan ya yi wannan furuci ne a ranar Laraba a wajen bikin tunawa da kuma gabatar da jawabin girmamawa ga Marigayi Edwin Clark, fitaccen shugaba daga yankin Ijaw.

An gudanar da taron ne a Abuja, inda manyan ’yan siyasa suka halarta.

Tsohon shugaban ƙasar ya ce batun mayar da Nijeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya yana tayar da ƙura a kafafen sada zumunta.

Jonathan ya ce ko da yake wasu ƙasashe sun rungumi tsarin jam’iyya ɗaya, an tsara hakan ne da kyau domin cimma wasu manufofin ƙasa.

Ya ce idan Nijeriya na da niyyar rungumar tsarin jam’iyya ɗaya, sai an tsara shi yadda ya kamata ta hannun masana da kuma bayyana manufofinsa.

By ukarofi