Na dauki matakai masu tsauri ne don mu samu ci-gaba, inji Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana tsauraran matakai da ya ke dauka wajen kawo gyara a harkar tattalin arzikin kasa a matsayin ababen da za su taimaka wa samun ci-gaba a Nijeriya.

Shugabannin ƙasar ya fadi haka ne a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja, ranar Juma’ar, a lokacin da ya karbi bakoncin wakili na musamman ga Sarkin ƙasar Ƙatar, Dakta Muhammada bin Abdul’aziz Al-Khulaifi.

Ya ce, kokarinsa na sauya fasalin haraji a kasar ya sanya masu zuba jari daga kasashen waje suna sha’awar yin kasuwanci a Nijeriya, domin hakan abu ne ya saukake masu hanyoyi shiga a dama da su.

A sanarwar da Kakakinsa, Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma ce sannu-a-sannu an fara ganin amfanin sauyin wanda nan ba da jimawa ba za a girbi cikakken amfaninsa acikin al’umma da ma kasa baki daya.

Da ya ke jawabi game da ziyarar babban wakilin, Tinubu ya ce alakar Nijeriya da Ƙatar za ta ginu ne akan karfafa bangaren abinci da kuma nasarori ga harkokin tattali.

Ya kuma ce, za su aiwatar da ababen ci-gaba na fannoni daban-daban da suka cimma matsaya a kansu a lokacin da ya ziyarci kasar a shekerar 2024.

Haka kuma, ya umarci wasu daga cikin ministocinsa da su hada kai wajen yin aiki tukuru don tabbatar da aiwatar da da ababen da ke cikin yarjejeniyar kasashen biyu.

By Babaji