EFCC ta kama ƴan Chana bisa zargin haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’an Hukumar Hana yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati, EFCC, sun yi nasar cafke wasu ƴan Chana biyu tare da ƴan Nijeriya shida kan hannu a aikata laifin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a yankin Ogere dake Jihar Ogun.

A sanarwar da Kakakinta, Dele Oyewale ya fitar, ya bayyana sunayensu kamar haka: Zhang Hang Lin, Gao Pei Hai, Matthew Mathias, Oluwaseun Amoo, Wasiu Ademola Alao, Ajibola Nurudeen, Ibrahim Yinusa, da kuma Saidu Shuaibu.

Ya ce, an kama su ne a ranar Juma’a a yayin wani atisaye, biyo bayan wani rahoton sirri da suka samu na ayyukan masu laifin.

Oyewale ya kara da cewa, daga cikin ababen da aka kwace daga hannun masu laifin akwai tireloli uku da aka cika su da wasu sinadarai da ake kyautata zaton hodar ‘lithium’ ce, wasu albarkatun kasa, mota kirar Toyota 4Runner SUV da wayoyin hannu.

Sauran sun hada da samfurin lithium mai ƙaramin karfi, katin cire kudi na ATM, fasfo-fasfo, da kuma fitilun hannu guda hudu.

Ya kuma ce, za a maka masu laifin a kotu bayan kammala bincike akansu.

By Babaji